Rahila Abdullahi" />

Kungiyar Sufiyya Ta Kasa Tayi Kira Akan Jaddada Zaman Lafiya

Wata kungiya me zaman kanta me suna Islahu Ummatus Sufiyya Tayi kira a kan jaddada Zaman lafiya a Kkasa baki daya.

Shugaban kungiyar, Alhaji Salihu Abdullahi (Mai-Barota) ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis din da ta gabata a lokacin da su ka kai ziyarar ban girma a ofishin dillacin labarai na Najeriya shiyyar Kaduna.

A lokacin da ya ke bayani, Alhaji Salihu ya ce, akwai hikima wurin halittar mutane da Allah ya yi cikin kabilu daban daban saboda mu san juna da kuma inda muka fito saboda a zauna lafiya da juna.

Ya kara da bayyana cewa, “Dalilin da ya sa muka kawo maku ziyara ta ban girma shi ne saboda karin dankon zumunta madawwamiya a tsakaninmu da ku.”

Ya cigaba da cewa, “mu na shaida mu ku cewar mun kawo maku ziyara ne ba tare da mun san ko ku Musulmai ne ko akasin haka ba, saboda muna ziyartar har wanda ma ba Musulmi ba domin addinin Musulunci ya nuna ma na mu zauna lafiya da kowa.

“Wannan kungiya tamu tana kai ziyara ga wurin pastoci da sauran shugabanni na addinin kirista domin burinmu shi ne samun hadin kai a cikin bangarori na kananan hukumomi, jahohi da kuma kasa bakidaya.

“Domin mun duba cewar idan ana samun ziyartar juna daga yare, addinai da kabiloli daban daban, za a samu fahimtar juna, wanda daga karshe zai haifar da zaman lafiya mai dorewa.”

Da ya ke nasa jawabin, manajan Arewa maso yamma na kamfanin dillancin labarai ta kasa, Alhaji Mahrazu Ahmed ya ce, ya yi farin ciki da zuwan wannan kungiya domin hakan na kara karfafa zumunci tsakanin al’umma.

Alhaji Mahrazu ya kara da cewa ita al’umma ba ta ginuwa idan babu zaman lafiya, amma an riga da an rarraba kawunan mutane ta bangaren addinai da kabilu, wanda hakan ba abu ne mai kyau ba.

Daga karshe ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su zauna lafiya ba tare da duba ga addini ko kabila da aka fito ba, a cewarsa.

Exit mobile version