Daga Mustapha Ibrahim Kano
Kungiyar Tsofaffin Dalibai ta ’yan mata ta Jogana wato Gobernment Girls Old Students Association tayi taro don hada kan tsofaffon dalibai da kuma taimakawa marasa karfi da kuma marayu a wannan lokaci kamar dai yadda shugabannin wannan kungiya Mallama Halima da Hajiya Sadiya jami`ar yada labarai ta wannan kungiya suka bayyana a wajen wannan taro a harabar makarantar AKCCC da ke garin Dutse suka bayyana a wajen wannan taron da ya gabata a wannan lokaci.
Taron wanda aka yi shi karkashin shugabancin mai taimaka wa Gwamnan Jahar Plateau Samon Lalong ta fuskar al`amuran mata watau Hajiya Umma Hassan Wayau, ta bayyana makasudin wannan taro da cewa, wannan wata dama ce ta ganin fuskoki da aka rabu shekara 22 zuwa 23 za a hadu a yi zumunci.To wannan abu ne mai kyau domin su a matsayinsu na wadanda suka kamala makaranta a 1994 bata sake ganin wasu ba sai a wannan taron, don haka abun farin ciki ne gasu tsofaffin dalibai na Jogana aji 94.
Haka kuma S.A Umma Hassan Wayau wacce ’yar asalin Kano ce wadda aure ya kaita Jos tayi amfani da wannan dama wajen shaidawa ’yan jaridu a matsayinta na siyasa tana amfani da wannan damar wajen hada kan al`umma musamman matan Jos wadanda kashi 85 cikin 100 masu yin kasuwanci ne da sana`a don haka ne ma gwamnati take taimakamasu ta fannoni daban-daban na sana`a kamar saka,dinki da sauransu. Wanda irin wadannan kayayyaki sun bazama cikin kasuwannin jahohin Najeriya daga Jos, inda kuma ta yabawa gwamna Lalong kan samun zaman lafiya wanda ta bada dama zama da tattaunawa a tsakanin Hausawa ’yan asalin Jos da baki da ma su kansu kabilu ’yan asalin Jos suma da bakinsu.
Inda shugaban makarantar ta Jogana Hajiya Asma`u Yakasai yabawa kungiyar tayi da kuma hukumomin ilimi na Jahar Kano a kan yadda ake gabatar da al`amura na ilimi, inda kuma ta jawo hankalin mahukunta da mawadata cewa, masallacin makarantar da sauran wasu wurare na cikin mawuyacin hali na lalacewa, hakanya sa suna gabatar da ibada cikin yanayi mara dadi da takura da ke bukatar agajin kowa da kowa.