kungiyar wanzamai ta kasa a karkashin jagorancin shugaban kungiyar mai rikon karya, Alhaji Rabo Sarkin Askar Kano, ta gudanar da gagarumin taro a Jihar Katsina a shiyyar karamar hukumar Funtuwa domin taya usman funtuwa murnar gudanar da taron addu’ar daurin auren dansa wanda ya gudana a harabar makarantar firamare ta Tudun Wada Funtuwa da ke cikin Jihar Katsina.
Taron kungiyar ta kasa wanda ya samu halartar manyan mutane da dama, daga cikin akwai sarakunan wanzamai na cikin jihohin kasar nan, tare da wasu daga cikin ‘yan kungiyar wanzamai ta kasa, kamar Alhaji Habibu sarkin askar kasar fambeguwa da ke cikin Jihar Kaduna, da Alhaji Buhari zariya sarkin askar zariya da ke wayanta baki daya da sauran su.
Sauran sun hada da Rabiu Iliyasu Tudun Wada Funtuwa, Usman Haruna Da Saidu Rabo, Surajo Wanzam Galadima, Sabiu Wanzam da dai sauransu.
Mai masaukin baki, shugaban kungiyar na karamar hukumar Funtuwa aura wanzan taron kungiyar wanzaman wanda ya kunshi wasanni daban-daban na masu sana’ar wanzanci da suka hada da yiwa kwarya kaho anan take kaga jini yana bulbulowa kamar ‘yan da ake kafama dan adam kaho jini ya fito da wasa da asaken aski da sauran wasannin wanzamai.
Ya ci gaba da cwa, “zan shawarci mambobin kungiyarmu da su cigaba da hada kai da juna tare da nemo hanyoyin da za su shigar da kungiyar tasu gaba kuma su zauna lafiya da sauran wanzamai abokan sana’ar su da sauran al’umma baki daya.”
Shima a nasa jawabin, mai masaukin baki kuma shugaban kungiyar ta wanzaman garin funtuwa, Auta wanzan, ya nuna jin dadin sa tare da yiwa manyan baki barka da zuwa wajen taron da zasu cigaba da gudanar da taron su na kungiyar wanzamai ta kasa, reshan kungiyar na garin funtuwa a cewarsa, da fatan Allah yasa ta tashi taron lafiya kuma ya mai da kowa gidansa lafiya.
Daga karshe aka ba PRO na kungiyar da ke garin funtuwa dama domin shima yace wani abu a game da kungiyar tasu ta wanzamai, inda ya bayyana cewa, zai yi iyakar kokarinsa wajen yada manufofin kungiyar domin cigar da ita gaba. Sauran wanzamai suma kowa ya tofa albarkacin bakinsa.