Muazu Hardawa" />

Kungiyar ’Yan Acaba Ta Nemi Tallafin Gwamnatin Jihar Bauchi

Kungiyar masu sufurin abin hawa ta acaba da keke napep na neman tallafin gwamnatin Jihar Bauchi wajen basu rancen abin hawa da biya cikin farashi mai sauki don kara samar da ayyukan yi tsakanin matasa a Jihar Bauchi.

Alhaji Abdullahi Mohammed Nabayi shugaban kungiyar ‘yan acaba da keke NAPEP na Jihar Bauchi shi ne ya bayyana haka inda ya kara nuna damuwa game da lamurran da ke faruwa ga mambobin sa don haka ya ke bukatar gwamnati ta taimaka musu musamman ganin yadda suka bayar da hadin kai wajen yin rijista da kuma kawo wannan gwamnati kan mulki, don haka suke bukatar gwamnati ta tallafa musu da keke napep da babura ko guda dubu daya domin su raba wa mutanen su.

Inda ya bayyana cewa sun ga abin da aka yi a Jihar Yobe inda aka raba musu keke dari shida da mashin dari shida kuma aka bukaci su biya rabin kudin an yi wannan a yawancin jihohin kasar nan an ci moriya amma jihar Bauchi ba abin da suka samu. Inda ya ce a 2016 gwamnati ta fara musu rijista kuma sun aminta sun bayar da goyon baya, amma son zuciya ya sa kudin da ake basu daga rijistar da kowane dan kungiya suka yi ba a basu duka ba lamarin  da ya kawo ci gaba amma su ba kudin da aka basu na alkawari wanda aka yi kan za a yi rijista a kan naira dubu uku kuma kungiya tana da naira dari uku kan kowane mamba kuma an yi rijistar sama da mutum dubu goma amma bai wuce na rabin mutanen aka basu ba don haka suke son gwamnati ta basu sauran kudin su.

Alhaji Abdullahi Nabayi ya bayyana cewa tun da aka bar rijistar ‘yan acaba mutanen sa na gamuwa da matsaloli masu yawa inda basa sanin mutanen da suka shigo cikin garin Bauchi don wannan sana’a kuma idan an kama su yawanci idan sun bi sawu sai su iske basu da rijista kuma yawanci baki ne daga Jigawa ko wasu jihohin na arewa da aka hana yin acaba a cikin su. Don haka ya bayyana cewa masu wannan sana’a suna gamuwa da hadurra masu yawa don haka ya kamata a ci gaba da musu rijista don tantance su.

Inda ya kara da cewa halin da ake ciki a Jihar Bauchi masu wannan sana’a na samun sassauci daga jami’an tsaro karkashin kungiyar su wacce a ko yaushe suke bin kadin mutane idan an kama su amma a wasu lokutan sai su iske wanda aka Kaman yawanci basu da rijista don haka suke son idan har an yi rijistar mutane su ci gajiyar shirin don kowa ya amfana daga gwamnati ta hanyar samun rance ko tallafin abin hawa da za su biya cikin farashi mai sauki. Don haka ya yabawa gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na Jihar Bauchi game da alkawurran day a musu kuma suke tuni don a cika musu suma su ci moriyar wannan gwamnati.

 

Exit mobile version