Daga Ahmed Muh’d Danasabe,
Ranan Juma’a 19 ga watan fabrairu,2021, rana ce da Sarkin Yakin Failar Lokoja, Alhaji Haruna Gimba( Baba Sarkin Makada) zai dade yana tunawa, domin kuwa a wannan rana ce wata kungiyar wacce ake kira kungiyar Yan Ataya dake Lokoja, ta karrama shi da lambar yabo a bisa dimbin gudun mawa da yake bayarwa da kuma hidima da ya dade yana yi wajen daukaka darikatul Tijjaniya da kuma dukkan lamuran da suka shafi Faila dama addinin musulunci a garin Lokoja da kewayenta.
Kungiyar ta baiwa Alhaji Haruna Gimba, wanda har ila yau shine Sarkin makadan Sarkin Lokoja lambar yabon ne a wajen bikin mauludin tunawa da ranan haihuwar manzon Allah, Annabi Muhammadu ( SAW) wadda kungiyar matasan Unguwar Kura ta shirya wadda ya samu halarcin daruruwan al’ummar musulmi dake birnin na Lokoja.
Shugabannin kungiyar sun bayyana wa wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU kadan bayan karrama Alhaji Haruna Gimba,cewa sun dade suna lura da irin hidimar da Sarkin makadan Sarkin Lokoja yake yiwa darikatun Tijjaniya musamman a wajen shirya bukukuwan mauludin Annabi Muhammadu ( SAW) da kuma addinin Musulunci.
A don haka kungiyar ta yi kira ga sauran al’ummar musulmi, musamman mabiya darikatul Tijjaniya da suyi koyi da Alhaji Haruna Gimba wadda ya sadaukar da dukiyarsa da kuma karfinsa wajen daukaka darikatul Tijjaniya da faila da kuma addinin musulunci a garin Lokoja da kuma kewayenta.
Da yake mayar da jawabi kadan bayan ya amshi lambar yabon wadda limamin masallacin Tudun Natsira, Alhaji Abubakar Adamu ya mika masa, Alhaji Haruna Gimba ya bayyana farin cikinsa da karrama shi da lambar yabon, inda kuma ya godewa kungiyar Yan Atayan a bisa tsamo shi daga cikin dubban musulmi da suma suke yiwa addinin musulunci dawainiya don karrama shi.
Ya ce, rana ce da ba zai taba manta wa a rayuwarsa ba, inda ya kara da cewa wannan ita ce karon farko a rayuwarsa da wata kungiya zata karrama shi, yana mai bayyana cewa karramawar zai kara masa kwarin gwiwar ci gama da yiwa darikatul Tijjaniya da kuma faila hidima.
Sarkin Yakin Failar ya kuma godewa mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji( Dr) Muhammadu Kabir Maikarfi na 111, a bisa goyon bayan da yake bashi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.