Daga A.A.Masagala Benin
A cikin wannan makon ne ‘yan kasuwa da aka fi sani da suna ‘yan baranda a babbar kasuwar shanu ta Benina Jihar Edo, suka zabi sabon shugabansu wanda zai maye gurbin tsohon shugabansu kana ya jagorance su a kan harkarsu ta baranda a babbar kasuwar.
Bayan takarar kujerar shugabancin a tsanin wasu mutum uku, wato Malam Hussaini Baba Damare da Alhaji Rabi’u sai kuma Malamu Musa Hamidu, inda a karshe Alhaji Rabi’u ya samu samu nasarar lashe zabe inda ya doke abokan takararsa da kuri’u 18.
Da yake zantawa da wakilinmu, sabon shugaban Alhaji Rabi’u, ya bayyana jin dadinda game da wannan nasarar da ya samu, tare da yin godiya ga Allah da kuma shan alwashin cewa zai kwatanta adalci a tsakanin duka mambobinsu ba tare da nuna wariya ko son kai ba.
Ya karasa da cewa, “Burina shi ne in ga mun hada kai a kan abin da zai kawo mana ci gaba da zaman lafiya a tsakaninmu da juna da kuma sauran jama’a, sannan ina jaddada kirana a gare mu da mu kasance masu gaskiya da rikon amana a harkokinmu baki daya.