Kungiyar ‘Yan Fansho Ta kasa Ta Karrama Gwamna Ganduje

Gwamnatin Kano

kungiyar ‘Yan Fansho ta kasa ta bai wa Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje lambar girmamawa a matsayin gwamnan da ya fi kowane amintaka da ‘yan fansho.

Kamar yadda Daraktan yada labaran mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hassan Musa Fagge ya Shaida wa LEADERSHIP A Yau

An baiwa Gwamnan lambar Karramawar ne a ranar Larabar data Gabata alokacin taron kungiyar Karo Na 11 na kungiyar ‘Yan Fansho wanda aka gudanar dakin taron rundunar sojojin sama dake Abuja.

Shugaban kungiyar ‘yan fanshon na kasa Dr. Abel Afolanya me ya bayyana haka a cikin jawabin da ya gabatar inda ya jinjinawa Gwamna Ganduje bisa taimakawa tare da tabbatar da biyan ‘yan Fansho hakkokinsu.

A cewarsa, ” wannan lambar Karramawa an yita ne ga Gwamna Ganduje bisa kyakkyawan jagorancin da yake a kasa tare da nuna farin cikin ‘yan fanshon Jihar Kano”,

Shugaban kungiyar’yan fanshon ya kara da cewa, “a watan October Shekarar data Gabata munje Kano domin bude Sakatariyar da Gwamnatin  Jihar Kano ta baiwa kungiyar.”

“kungiyar ‘yan fanshon Jihar Kano sun jaddada  cewa Gwamnan su mai sauraro ne,  kuma wani abin sha’awa shima dan Fansho ne kuma mutun ne da ya damu da al’amarin al’umma.” Ko shakka babu wannan Karramawa da aka Yi masa na Gwamna mai kyakkyawan jagoranci da Kuma haba haba da ‘yan Fansho ta Dace kwarai da gaske.

Da yake gabatar da jawabinsa Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje wanda mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya wakilta ya godewa kungiyar ‘yan fanshon ta kasa bisa wannan lambar Karramawar, wanda yace abin alfahari ne Kwari da gaske ga Gwamnatin Jihar Kano Wanda zai karawa Gwamnan kaimi wajen kyautata rayuwar ‘yan fansho a Jihar Kano.”

“Ina matukar alfahari da wannan kungiya kuma Ina fatan ci gaba  da goyon bayan harkokinsu domin tabbatar da samun nasara, Inji Ganduje.”

Ya kara da cewa, Gwamnatinsa bata taba yin fashin biyan ‘yan Fansho na wata wata ba tun zuwanta a Shekara ta 2015 zuwa yau.

Haka Kuma Gwamnan ya jinjinawa kyakkyawar dangantakar dake gudana tsakanin  Gwamnati da ‘yan fanshon Jihar Kano. Don haka ya tabbatar cewa nan bada jimawa ba Gwamnatinsa zata biya dukkan hakukuwan ‘yan Fansho.

Sauran manyan baki da suka tofa albarkacin bakinsu sun hada da  Ministan  ma’aikata da kwadago, Dakta Chris Ngige wanda babban sakataren Ma’aikatar ya wakilta,  Shugaban Kwamitin harkokin ma’aikata na Majalisar dattijai Sanata Malam Ibrahim Shekarau da  Shugaban kungiyar kwadago na kasa Kwamared Ayuba Wamba.

Abubuwan da aka gudanar alokacin taron bada lambar Karramawar sun hada da Gwamnan Jihar Legas, Yobe, Borno da Jihar Oyo duk Suma an karrama su sakamakon Jajircewa tare da gudunmawar da suke ga kyautata rayuwar ‘yan fanshon.

Exit mobile version