Husaini Sulaiman" />

Kungiyar ’Yan Jaridar Jihar Kano Ta Ja Kunnen ’Yan Siyasa

Kungiyar ‘yan jarida ta jihar Kano karkashin jagorancin Kwamred Abbas Ibrahim ta gargadi tare da jan haukulan manya da kananan ‘yan siyasar jihar Kano, da su guji munanan kalaman da zasu iya haifar da tashin tashina ganin yadda ake karab gudanar da zaben 2019.

Wannan kalamin ya fito ne bayan kammala taron da kungiyar ta saba gudanarwa duk karshen wata a cibiyar ‘yan jarida dake gidan Gona a Kano, inda ya samu da dama daga cikin ‘yan kungiyar.

Shugaban kungiyar ya ci gaba da cewa, ya zama wajibi ‘yan jarida su kaucebwa yada labarai marasa inganci ko kuma wadanda zasu kawo rashin zaman lafiya a jiha ko a kasa baki daya.

Sannan kuma yana da kyau su rika fadakar da ‘yan siyasa muhimmancin siyasa ba da gaba ba. Kwamared Abbas Ibrahim da sakataren kungiyar Abba Murtala, sun kara da cewa su kuma gujewa yada labarai da ba su ta tabbas musamman wadanda al’umma ke yadawa a kafofin sada zumunta irin na zamani.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kafa hukumar da zata rika hukunta masu safarar miyagun kwayoyi a jihar kamar yadda ta kafa na masu ruf da ciki da dukiyoyin jihar. Taron ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Kano game da aikace aikacen raya kasa da ake gudanarwa a fadin jihar ta Kano,

Daga karshe kungiyar ‘yan jarida ta taya sakataren kungiyar Kwamared Abba Murtala a bisa sanya shi a matsayin daya daga cikin ‘yan kwamitin da zasu gudanar da zaben kungiyar ta kasa.

Exit mobile version