Kungiyar ‘Yan Kasa Ta Karrama Matar Gwamnan Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

kungiyar ‘Yan Asalin kasa watau (Indigenous Organization) ta girmama matar gwamnan Jihar zamfara, Hajiya Aisha Bello Mattawalle da lambar yabo sakamakon ayyukan ci gaban da ta samar a jihar.
Sakatariyar yada labarai ta Matar Gwamna, Zainab shu’aibu Abdallah, ce ta bayyana haka a takardar da ta sanya wa hannu ta raba wa manema labarai a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.
Zainab Shu’aibu ta bayyana cewa, lambar yabon ta dogara ne da irin gudummawar da ta ke ba wa mata a Jihar wajen inganta rayuwar mata ta kowane fanni.
lanbar yabon wacce kungiyar ta ‘Indigenous Organisation NGOs’ ta bata, an ba ta ne saboda irin gudummawar da take bayarwa tare da jajircewarta wajen bunkasa rayuwar al’ummar mata da ya hada da ilimin, lafiya, kananan yara, gami da taimakawa gajiyayu da bayar da jari ga masu kanan sana’o’i da Naira Naira 20,000 a kowane wata da sama da mata 1,800 suka amfana da shi a fadin kananan hukumomin 14 da ke fadin Jihar ta Zamfara.
An zabi matar Gwamnan tare da matar Gwamnan Gombe Kaduna da Kwara a matsayin wadanda suka fi cancanta da kyautata wa al’umma saboda kishinsu na jihar.
“Masu ba da lambar yabon, suna mai da hankali kan manyan matan shugabanni wadanda ke da zuciyar ci gaban mata da matasa da yara kanana wadanda su ne idan rayuwar su ta inganta al’umma ta inganta.
Akan haka ne Sakatariyar yada labaran ta jinji wa kungiyar da kuma godiya a gare ta bisa karrama Hajiya Aisha Matawallen Maradun, don kara mata kwarin gwiwa wajen ci gaba da ayyukan da ta sa gaba na inganta rayuwar al’ummar Jihar Zamfara.

Exit mobile version