Kungiyar ‘yan kasuwa Ta Kaurace Wa Yajin Aiki A Zamfara

Daga Sagir Abubakar

Kungiyar ‘yan kasuwar jihar Zamfara ta turje da kaurace wa yajin aikin kungiyar kwadago ta bada umarni a fadin jihar. Shugaban matasan ‘yan kasuwar kuma mataimakin shugaban Cibiyar kasuwanci na jihar Alhaji Mustafa Ma’azu Walin Kwatarkwashi, ne ya bayyana wa Leadership A yau haka a lokacin da ke zanta wa da wakikinmu a shagonsa da ke tsohuwar kasuwar Gusau.

Walin Kwatarkwaahi ya bayyana cewa “kungiyar kwadago ta jihar Zamfara ta shigo kasuwa don rufe ta mu mara masu baya muka ce haka bat a sabu wa bindiga a ruwa, don kuke da matsala da gwamnatin ba mu ba”.

A nan ne Walin ya yi musu waiwaye adon tafiya a kan kin mara musu baya inda ya bayyana cewa” a zangoan farko na gwamna Yari, gwamnatin tarayya ta bai wa’‘yan kasuwarmu biliyan biyu don bunkasa kasuwanci da kudin suka makale muka nemi gudunmowarku don kudin su fito babu wani tallafin da kuka ba mu, sai da gwamnan Jigawa na yanzu Alhaji Badaru lokacin shi ne shugaban Cibiyar Kasuwanci ta kasa ya zo har Gusau ya tsaya tsayin daka sai da ya ga gwamna Yari ya  ba mu wadannan kudaden”. Kuma sanda tsohun gwamnan Zamfara na mulkin Soja Kanal Jibiril Bala ya nemi tashinmu a wannan kasuwa muka tsaya kai da fata har da zuwa kotu babu gudunmowar kungiyar Kwadago. Don haka, babu dalilin da zai sa mu kulle kasuwa don biyan bukatun wasu .

A kan haka nake kira ga ‘yan Kasuwarmu da kowa ya saki jiki ya ci gaba da harkar kasuwancinsa.kuma mu ci gaba da ba gwamnatin gwamna Abudulaziz Yari hadin kai da goyan baya don kudirita ya hakaku na ci gaban jihar.

Exit mobile version