Connect with us

MANYAN LABARAI

Kungiyar ‘Yan Kasuwa Za Ta Fara Yajin Aiki Ranar Alhamis

Published

on

Kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), ta ce tana nan akan bakarta na fara yajin aikin da ta daura anniyar yi karkashin kungiyar kwadago a ranar Alhamis din jibi, bayan abinda kungiyar ta kira saba alkawarin da gwamnatin tarayya ta yi na kin aiwatar da mafi karancin albashi a ranar 27 ga watan Satumba, kamar yadda gwamnatin ta yi alkawari a baya.

A cikin takardar da babban sakataren kungiyar, Mista Musa-Lawal Ozigi, ya sanya wa hannu, na dauke da shawarar da kwamitin kungiyar na kasa ta zartar a ranar 24 ga watan Satumban nan.

Ozigi ya ce, mun zartar da zamu shiga yajin aiki a ranar Alhamis 27 ga watan Satumba 2018, kuma zuwa yanzu duk mun shirya mambobin tsaf don shiga yajin aiki, duk ma’aikatan gwamnati, kungiyoyin fararen hula, da kuma sauran jama’ar kasa yakamata su tara kayan masarufinsu a gida saboda yajin aikin.

Kungiyoyin kwadagon sun gargadi gwamnatin tarayya da ta kiyaye jan kafa akan batun kin aiwatar da mafi karancin albashin, sannan ta kyale kwamitin ‘yan uku da aka kafa don duba batun mafi karancin albashin ya yi aikinshi, ba tare da sa hannun gwamnatin ba.

Shugaban kungiyar kwadago Mista Ayuba Wabba, ya ce sam kwamitin bai ji dadin kalaman da ministan kwadago Dakta Chris Ngige ya furta ba, inda ministan ya bukaci kwamitin ya jan tattaunawar da yake har sai sun kare tattaunawa da gwamnatin tarayya.

Duk da gwamnatin tarayya ta tabbatar wa kungiyoyin kwadago cewar lallai kwamitin ‘yan uku zai gama muhawara akan batun kafin wa’adin kwana 14 da ‘yan kwadagon suka bayar wa gwamnatin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: