Ahmed Muhammad Dan Asabe" />

Kungiyar ‘Yan Kasuwar Arewa Reshen Kogi Ta Yaba Wa Gwamna Bello

kungiyar Yan Kasuwar Arewa Reshen Kogi Ta Yaba Wa Gwamna Bello
Daga Ahmed Muh'd Danasabe, Lokoja
kungiyar
yan kasuwa ta arewacin Nijeriya (Arewa Traders Association), ta yaba wa wamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Adoza Bello bisa kudurinsa na raya jihar da samar da cikakken tsaro da kuma goyon da yake bai wa kungiyar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Shugaban kungiyar na jihar Kogi, Dakta Umar Muhammed ne ya yi yabon a yayin da yake zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a, a jiya a birnin Lokoja.
Dakta Umar Muhammed ya bayyana Gwamna Bello a matsayin shugaba jajirtacce,haziki, mai hangen nesa kuma dan kishin kasa wanda ya kuduri aniyar kyautata rayuwar al’ummarsa.
Shugaban kungiyar wanda har ila yau shi ne sakataren jin dadi da walwala na kungiyar a jihohin arewa ta tsakiya ya kuma yi kira ga Gwamna Bello daya kara kokari da kuma himma  don ganin jihar Kogi ta cimma takwarorinta irinsu jihohin Legas da Ribas da Kano da kuma sauran jihohin da suka ci gaba a kasar nan.
” A matsayina na shugaban kungiyar yan kasuwan kuma sakataren jin dadi da walwala na kungiyar mai kula da jihohin arewa ta tsakiya da suka hada da Kogi, Neja, Binuwe, Nasarawa, Kwara, Filato da kuma babban birnin tarayya( FCT) Abuja, zan yi amfani da wannan dama a madadin kungiyar wajen kira ga mai girma gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Adoza Bello, daya kara kokari,azama da kuma himma da yake yi na tabbatar da ganin gwamnatinsa mai albarka ta samar da ci gaba mai ma'ana, fiye da yadda ake samu yanzu a jihar.
"Jihar Kogi,jiha ce mai wahalar shugabanta,domin kuwa kowace yare ko kabila na ikirarin ita ke da Kogi. Saboda haka shugabancin jiha kamar kogi, sai mai hakuri, ilimi, basira da kuma dattako wanda ya san dai dai gwargwadon rayuwa irin gwamna Bello.
" A don haka nake kira ga gwamnan daya kara kokari da himma da kuma nuna dattako da yake yi wajen tafiyar da akalar jihar Kogi.
" Dan Adam, ba a iya masa, wani ko me kayi masa na kyautata wa, babu yadda zai yabe ka, amma mu kungiyar
Yan kasuwa ta Arewa Traders Association, mun ga kokarin da Gwamna Yahaya Adoza Bello yake yi a jihar Kogi na raya sassa daban daban na jihar “inji Dakta Muhammed.
“Har ila yau, zan yi  amfani da wannan kafa wajen jinjina wa gwamnan a bisa tashi haikan don samar da tsaro ta hanyar yaki da ayyukan aikata laifufuka da suka hada da satar jama’a da fashi da makami da kungiyoyin asiri da dai makamantarsu,wadanda hakan ya sa jihar Kogi tana kan gama a wajen samun zaman lafiya a duk fadin kasar nan.”
Shugaban kungiyar ya kawo misalin  mahadar Ganaja( Ganaja Junction) dake birnin Lokoja, wacce a yanzu gwamnatin jihar ta ba da kwangilar gina katafaren gadar sama, wato Fly Ober a mahadar, wanda idan an kammala shi zai rage cunkoson ababen hawa da kuma hadarurukan dake faruwa jifa jifa a wajen da giggina wa da yi wa asibitoci da makarantun jihar kwaskwarima da samar da ruwan sha a birane da kuma yankunan karkara da samar da ayyukan yi ga matasa da kuma shigar da mata cikin harkar siyasar jihar domin suma su san ana
damawa dasu a matsayin kadan daga cikin ci gaba da gwamnatin Yahaya Adoza Bello ta cimma a jihar ta Kogi.
” Muna yi wa Gwamna Bello addu’ar Allah yasa ya gama lafiya. Haka kuma,duk da cewa mu kungiyar mu bata siyasa bace, mun Yan kasuwa ne,amma kuma muna jaddada goyon bayan mu ga kudurin sa na neman shugabancin Nijeriya, wato ma'ana kungiyar mu tana goyon bayan tsayawarsa takarar shugaban kasa a 2023 In sha Allah. Muna addu’ar Allah ya bashi sa’a ya zama shugaban kasa domin Nijeriya ta canza da kuma ganin ta samu ci gaba kamar sauran manyan kasashen duniya da suka ci gaba a fannoni daban daban.” A cewarsa.
Dakta Umar Muhammed har ila yau ya jinjinawa gwamnan a bisa gina gidan tara kudaden shiga na cikin gida( Rebenue House) da nufin tara kudaden cikin gida da jihar za ta rika amfani dasu wajen gudanar da ayyukan raya kasa.
Sai dai kuma ya shawarci wadanda ya danka wa amana, wato hadimansa dasu rike amanar tare da yin abubuwan da suka dace domin taimaka wa gwamnan da kuma al’ummar jihar tare da ganin gwamnan ya samu nasarar sauke nauyin da jama’ar jihar suka dora masa.
“Kowa ya tuna cewa zai bada ba’asi a gaban Allah a ranan tashin kiyama game da amanar da aka damka masa” Dakta Umar na mai nanata wa.
Hakazalika, shugaban kungiyar `Yan kasuwar ta Arewa Traders Association, reshen jihar Kogi, Dakta Umar Muhammed ya jaddada goyon bayansa ga gwamnan akan dagewa da yayi na cewa ko kadan babu cutar sarkewar numfashi ta korona a jihar Kogi, inda yace idan akwai cutar, da tuni an gano mai dauke da ita a jihar.
A don haka, ya shawarci hukumar yaki da cutttuka ta kasa (NCDC) da ta daina kokarin kakabawa jihar Kogi cutar da ba ta da ita.

Exit mobile version