Balarabe Abdullahi" />

Kungiyar ‘ZEMDA’ Ba Batun Tsaro Kawai Mu Ke Yi Ba -Alhaji Ahmad Maccido

‘’Tun da aka kafa KUNGIYAR CI GABAN MASARAUTAR ZAZZAU [ZEMDA], mun sa abububwa da dama da suka shfi ciyar da masarautar Zazzau gaba, ba a batun tabbatar da tsaro mu ka saw a gaba kawai ba’’ Shugaban wannan kungiya , Alhaji Ahmad Maccido ya bayyana haka a

zantawarsa da wakilinmu da ke Zariya jim kadan bayan sun kammala taron kungiyar day a gudana a ofishin kungiyar da ke Zariya.

Alhaji Ahmad ya ci gaba da cewar sun yi wannan taron ne domin yin waiwaye adon tafiya na ayyukan da kungiyar ta gudanar da nasarorin da ta samu da matsalolin da ta samu wajen ayyukan da kungiyar ta aiwatar a baya da kuma ayyukan da za ta aiwatar a nan gaba.

A game kuma da yadda kungiyar ke aiwatar da ayyukanta, Alhaji Ahmad Maccido ya ci gaba cewar, kungiyar na da ofisoshi a daukacin kananan hukumomin da suke masarautar Zazzau, amma, kamar yadda ya ce, kungiyar na da babban ofishinta a Zariya.

Sauran ayyukan da wannan kungiya ta [ZEMDA] ke aiwatarwa sun hada da batun tallafa wa matasa na samar ma su yadda za su ci gaba da karatu a ko wani mataki na ilimi dad a kuma tsaron lafiyar al’ummar masarautar Zazzau da kuma dukiyarsu.

Sai dai kuma ya bayyana cewar, al’umma sun fi sanin kungiyar da batun tsaro, wannan ya faru ne a dalilin yadda ‘ya’yan kungiyar ke ayyuka tukuru day a shafi tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma dare da kuma rana a masarautar Zazzau.Kuma ayyukan wannan kungiya sun fito fili ne a dalilin ayyukan ‘yan baya ga dangi da suke Unguwar Jushi, a birnin Zariya, wanda zuwa yanzu, a cewarsa, sun sami nasarori ma su yawan gaske.

Wannan matsala na yadda matasan Jushin birnin Zariya ke neman mayar da Unguwar wani fage na tashin hankali,wanda ya sa al’ummar da suke da gidaje a yankin sai sayar da gidajen suke yi, suna barin Unguwar, amma yanzu, an sami zaman lafiya dauwamamme a wannan Unguwa ta Jushi da kuma Sabon garin Zariya da sauran wurare da suke masarautar Zazzau.

Alhaji Ahmad Maccido ya kara da cewar, zuwa yanzu wannan kungiya na da matasa da aka ba su horo na musamman kan tsaro su fiye da dari biyu, da suke aiki a karkashin wannan kungiya a daukacin kananan hukumomin da suka hadu, a karkashin masarautar Zazzau, wanda in za su fita aiki suna fita a wasu lokuta tare da ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro na hukuma.

A bangaren ilimi kuma, Alhaji Ahmad ya ce wannan kungiya ta su, sun bayar da gudunmuwa mai yawa ga yadda aka sami shawo kan matsaloli a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, wanda wannan batu a bayyane yak e ga wadanda suka sani.

A karshen ganawar wakilinmu da Alhaji Ahmad Maccudo ya yi kira ga al’ummar masarautar Zazzau, da su ci gaba dab a wannan kungiya duk goyon bayan da suka da ce, domin kungiyar ta sami damar aiwatar da ayyukan da ta saw a gaba da suka shafi ilimi da tsaro da sauran abubuwa da za su ciyar da masarautar Zazzau gaba.

Exit mobile version