Gasar Premier ta bana a bude take, bayan da kawo yanzu kungiyoyi hudu ko biyar ne ake saran wata a cikinsu za ta iya lashe kofin sakamakon yadda ake gudun yaya da kann wani a rige-rigen zama na daya akna teburin gasar.
Ya zuwa yanzu maki tara ne tsakanin kungiyar farko da ke kan teburi zuwa ta bakwai, saboda haka sai nan gaba ne fitila za ta nuna wadda za ta ci Premier League amma kawo yanzu kowacce kungiya zata iya zama ta daya.
A baya sai kaga kungiya ta bayar da tazarar maki tsakaninta da sauran kungiyoyi kamar yadda Liverpool ta lashe Premier a bara da tazarar maki 18 sai dai a wannan kakar kungiyoyin gaba daya basa irin kokarin da sukayi a baya.
Liverpool wadda a bara ta lashe Premier yanzu tana ta hudu a teburi, koda yake ta ci karo da koma baya, yayin da wasu fitattun ‘yan wasanta ke jinya sannan Manchester City wadda ta yi ta biyu a bara yanzu tana ta daya, bayan wasanni 19 da ta buga.
Manchester United wadda ta buga Champions League na bana aka yi waje da ita ta barar da damar komawa ta daya a teburi, bayan da Sheffield United ta doke ta 2-1 ranar Laraba har filin wasa na Old Trafford.
Chelsea wadda ta samu gurbin Champions League ta koma ta 10 duk ka cefane mai tsada da ta yi kuma rashin kokarin Chelsea ya sa ta sallami Frank Lampard tare da nada Thomas Tuchel kan yarjejeniyar watanni goma sha takwas.
Eberton da ta fara kakar bana da kafar dama ta koma ta bakwai a teburi, bayan da ta tashi kunnen doki da kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ranar Laraba karawar mako na 20 ya yinda ita Leicester City wadda ke yin abin azo a gani yanzu tana ta uku, za kuma ta taka rawar da za ta bai wa kowa mamaki.
Tottenham ma tana daga cikin kungiyoyin da ake sa ran za ta bai wa marada kunya wadda ta kara da Liverpool ranar Alhamis kuma tayi rashin nasara daci 3-1 a wasan da dan wasa Harry Kane ya samu ciwo.
Arsenal ma wadda yanzu ta shigo cikin ‘yan taran farko ana sa rai ganin yanzu ta koma kan ganiya, bayan da a baya ta dade a mataki na 15 a kasan teburi kuma har aka fara rade radin zata iya faduwa daga gasar firimiya.
Ya zuwa yanzu kungiyoyi tara ne suka hau teburin gasar Premier suna kuma sauka, kuma da yiwuwar anan gaba a samu ta goma ko sama da haka idan har wasanni suka ci gaba da afiya a haka.
Za A Yi Kare Jini Biri Jini Tsakanin Real Madrid Da Atletico Gobe
A ranar Lahadi ne Real Madrid za ta ziyarci filin...