Haruna Akarada" />

Kungiyoyin Dambatta ‘Charity’ Sun Karrama Masu Kwazon Cikinsu

Dambatta ‘Charity’

Kungiyoyin Dambatta Charity Foundation, da Dambatta Academic Forum sun samu zama na wuri guda da Shugaban hukumar sadarwa ta kasa (NCC) Farfesa Umar Garba Dambatta, a sabon ofishinsa dake Kano. Domin tattauna al’amuran da suka shafi al’ummar karamar hukumar.

A wata dama daya basu domin jin ta bakinsu, inda aka kwana da inda za a tashi, a batun da ya shafi cigaban al’ummar wannan yanki baki daya.

Shugabannin kungiyoyin 2, Alhaji Nasiru Danguda da kwamared Sulaiman Ibrahim (Baffale) sun yabawa Farfesan a bisa gudummawar da yake bayarwa domin cigaban al’umma, musamman a kan sha’anin tsaro, lafiya da ilimi, walwalar jama’a, koyar da sana’a, samar da guraben aiki a ma’ikatu da kamfanoni tare da gabatar masa wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da walwalar jama’a, taimakawa dalibai, samar da aikin yi, ayyukan cigaba na raya kasa da sauransu.

Farfesa Umar Garba Dambatta ya jinjinawa tagwayen kungiyoyin biyu, a bisa irin gudummawar da suke bawa al’umma, tare da karbar dukkan shirye-shiryen da suka mika masa. Har ma ya bada umarnin a fara gabatar da wasu daga cikin abubuwan da suka mika masa a kwana kusa, a yayin da sauran ma ya ci alwashin zai bisu daya bayan daya

A karshe an gabatar masa da kyaututtukansa na karramawa da ya samu daga Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jiha CP Habu Sani, da na Salka Media, da kuma na Injiniya Hamisu Ibrahim Yarima (Duniya ba hutu). Mina

Exit mobile version