Abdullahi Muhammad Sheka" />

Kungiyoyin Fulani Ta Afirka Ta Zabi Ganduje A Matsayin Uban Kungiyar Na Afirka Baki-Daya

Gamayyar kungiyoyin Makiyaya na fadin Tarayyar Turai da Amurka, sun zabi Gwamnan Jihar Kano, Daktar Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin Uban kungiyar, wanda shi ne guda daga cikin ‘ya’yan kasashen Afirka na farko da ya taba rike wannan mukami.
Haka zalika, karkashin inuwar gamayar kungiyoyin cigaban Makiyaya da zaman lafiya, wadda ke da shelkwata a lamba ta 12121, titin Audia Apt 2308 Dallas Td 75243, USA, wadda kuma ke da matsuguni a nan Nijeriya, a lamba 4 Sambo Close, Badiko, ta Jihar Kaduna, kungiyoyin sun jinjinawa Gwamna Ganduje bisa kyakkyawar aniyarsa akan harkokin cigaban Fulani a Lardin kasashen Afirka.
Bayanin haka, na kunshe ne cikin wasikar da aka aikawa gwamnan, domin sanar
da shi wannan zabi da aka yi masa, wanda Babban Sakataren kungiyar, Mohamamed Farouk Auwal, ya rattabawa hannu. Kamar yadda wasikar ta bayyana, “mai girma Gwamnan Jihar Kano, kokarin da gwamntinka ke yi domin magance matsalolin Makiyaya a Nijeriya, babu shakka abu ne wanda ya dauki hankalin kowa da kowa tare da jan hankalin wannan kungiya, sakamakon wannan dalili ne yasa muke rokonka ka amince da zama Uba ga wannan kungiya.”
Har ila yau, “a cigaba da kyakkyawar aniyar Gwamna Ganduje, na samar da matsugunin RUGA ga Makiya, yasa muke neman gwamna ya ba mu dama, domin tattauna wadannan muhimman batutuwa da shi, musamman al’amuran da suka shafi harkokin Makiyaya da kuma sabon tsarin samar da Burtali, tare da bayar da shawarwari akan yadda za a samar da tsarin cikin sauki ga su Fulani.”
Wasikar ta cigaba da bayyana cewa, kasancewarmu na kungiya, muna da kyakkyawan hange da kuma mafita ga harkokin Makiya da ke tafiye-tafiye a fadin yankunan kasashen Afirka. “Kamar yadda muke fatan bujiro da dabarun samar da wuraren kiwo da Burtalai a Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka baki daya.
Haka zalika, sun tunawa Gwamnan cewa, “akwai bukatar hadin kai tare da mu don yin aiki tare domin ragewa gwamnati wani nauyi na daban, sannan muna tabbatar da wannan bukata tare da neman amincewarka, wanda hakan zai kara tabbatar da kyakkyawar kulawar da ke zuciyarka.”
“Mu a matsayinmu na Makiyaya kuma Fulanin Afirka, masu rajin samun zaman lafiya da cigaba, mun zabe ka domin sanin matsayinka da kuma nuna kyakkyawan jagorancin da kake nuwa a cikin gwagwarmayarka ta yau da kullum, domin cigaban karanana Makiyayanmu na fadin Afirka baki-daya. Mutumin da ya damu tare da amincewa da yin yaki don samun nasarar Fulani a kowane sassa na fadin Afirka.”
Haka nan, da suke kara bayyana amfanin da za a samu, sakamakon nadin Ganduje
a matsayin Uban wannan kungiya, cewa suka yi, “wannan a bayyane yake samun
irinsa a masayin Uban kungiya, zai kara karfin ayyukan kungiyar a fadin Afirka da kuma inganta kokarin kungiyar na yaki tare da kare kimar Makiyayan yankunan na Afirka.”
Haka zalika, “za a gudanar da wannan tsari ne ta hanyar hadin kai, kyautata alaka da kuma hadin guiwa tare da dukkanin Gwamnonin Arewa, Hukumomin cigaba na duniya da sauran masu ruwa da tsaki cikin wannan gwagwarmaya. Muna da cikakken tabbacin cewa, Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, zai tabbatar da ingantaccen jagoranci wajen samun nasarar aikace-aikacen kungiyar.” Kamar yadda Babban Darkatan Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya shaida wa Jaridar Leadershiap A Yau Asabar.

Mutum Miliyan 7 Ke Da Bukatar Agajin Gaggawa A jihar Borno Da Adamawa Da Yobe- In Ji Un
Daga Muhammad Maitela, Borno
Majalisar dunkin duniya ta bayyana damuwar ta dangane da halin da al’umma sama da miliyan bakwai su ke ciki a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, na matsin rayuwa, karancin abinci, ta dalilin bahallatsar rikicin Boko Haram, wanda ya dace a dauki kwakkwaran matakan shawo kan lamarin.
Majalisar hada hancin kasashen duniya, ta yi wannan furucin a cikin wata sanarwar bayanai wadda ta fitar, a ranar Jumu’a, ta hanyar ofishin babban sakataren kula da lamurran ayyukan jinkai da tallafin gaggawa, Mista Mark Lowcock, yayin da fara da cewa, “yau kimanin sama da shekara guda, ina mai kula tare da shiga cikin damuwa dangane da yadda wannan matsalar ke dada kamari a nan jihar Borno”.
“Bayan shekaru goma da fara wannan rikici na Boko Haram da sauran matsalolin tsaro da ke da alaka dashi, wanda ya tagayyara yankuna da dama. Wanda ziyarata zuwa Borno, cikin watan Satumba na 2017 da Octoban 2018, na samu damar zanta wa da jama’ar gari da yawa, wadanda matsalar ta shafa kai tsaye, wanda ko tantama babu, akwai kimanin mutum sama da miliyan bakwai wadanda ke neman daukin tallafin gaggawa- wurjanjan, a jihohin Borno, Adamawa da Yobe”.
“Kuma mun yaba da kokarin da mahukuntan Nijeriya tare da wasu kungiyoyi ke yi, dangane da lamarin, tsakanin shekarar 2016 da 2018, wajen sake kwato wasu yankuna daga hannun mayakan, al’amarin da ya tilasta mutum sama da miliyan biyu yin hijira, inda suka koma gudajen su. Amma kuma ta dalilin sake rincabewar tsaron, ta kai sabbin hare-haren maharan Boko Haram din, ya kara sanya fargaba a zukatan jama’ar jihar Borno, wanda aka samu sabbin yan gudun hijira sama da 140,000, a wannan shekarar kawai. Hakan ya jawo dubun-dubatar basu samu damar yin noma a wannan damina ba, lamarin da ya jefa mutane sama da miliyan uku a cikin matsalar karancin abinci”.
“Kuma karara zan iya bayyana cewa, matakan da sojoji tare da hadi da sauran jami’an tsaro ke dauka wajen yaki da matsalar tsaro, ya zama dole kuma shi ne matakin da ya dace mahukuntan Nijeriya su dauka. Kuma dole sojoji su kula da jama’a a duk lokacin da za su aiwatar da wani matakin yaki da yan ta’addan; wajen kiyaye abubuwan da duk zai jefa jama’a cikin tsananin rayuwa”.
“Sannan kuma, matakin soja shi kadai ba zai iya shawo kan wannan matsalar ba. Saboda haka, bisa wannan, akwai mashahurin muhimmanci gwamnatin Nijeriya ta bullo da wasu karin hanyoyin da zasu taimaka a yaki matsalar, misali a shigar da hukumomi da cibiyoyi, irin su hukumar sake bunkasa yankin arewa maso gabas, wajen fadada bin hanyoyi da manufofi tare da tunkara musababbi da asalin hargitsin, rage wa jama’a radadin wahalhalun rayuwa da suka dabaibaye jama’a, bunkasa yankunan, sake farfado da lamurra da ci gaban jama’a, wanda ko shakka ba na yi, idan an dauki wadannan matakan, zai haifar da da mai ido”.
“Na yi farin cikin yadda na sake samun damar kawo ziyara a nan jihar Borno a wannan makon, lamarin da ya bani dama wajen sake bin bahasin yadda abubuwa ke gudana, tare da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya, jami’an rundunar sojoji, da manyan jami’an gwamnatin jihar Borno, da sauran kungiyoyin agajin jinkai na kasa da kasa, na cikin kasa da kananan masu bayar da tllafin, a kokarin su wajen ganin ayyukan su sun shiga kowane lungu da sakon jama’a- a hakikanin gaskiya suna taka muhimmiyar rawa”.
“Saboda haka, majalisar dunkin duniya tare da hadin gwiwa da ofishin hukumar kula da ayyukan jinkai, suna bayar da dukan goyon bayan da duk ake bukata wajen samun nasarorin ayyukan tallafin da kungiyoyi ke yi a yankin arewa maso gabashin Nijeriya, tun farkon barkewar rikicin. Wanda a shekarar 2019 kadai, sun gudanar da aikin ceton rayukan jama’a sama da mutum miliyan uku da digo takwas (3.8 m).
Ya ce, wadannan kungiyoyin suna gudanar da ayyukan su kome runtsi da wahala. Ya kara da bayyana cewa, “akwai adadin ma’aikatan majalisar dunkin duniya 38 tare da sauran kungiyoyin jinkai da aka kashe tun daga 2011, wadanda mafi akasarin su yan Nijeriya ne. Sannan da karin wasu ma’aikatan bayar da agaji goma da rikicin Boko Haram ya rutsa dasu, watani 18 da suka gabata, inda guda takwas suka yi batan-dabo”.

Exit mobile version