Connect with us

WASANNI

Kungiyoyin Ta’adda Na Amfani Da Yanar Gizo Wajen Samun Mabiya

Published

on

Jami’an Amurka da suke yaki da ta’addanci sun ce duk da irin nasarori da aka samu a yaki da ta’adanci da sake kwato yankunan daka hannun kungiyoyin ta’adda kamar ISIS da Al Ka’ida, yanayi da harkokin ta’adanci sun kara sarkakiya.

Kungiyoyin ISIS da Al-kaida da kawayen su, sun nuna suna kan bakarsu, da nuna juyriya, da badda sawu” a cewar wani babban jam’in yaki da ta’addanci Nathan Sales a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa kungiyoyin sun sun sauya take takensu saboda kara matsa kaimi wajen yaki da ta’addanci a Iraki da Somalia da sauran wuraren da abin ya shafa.

Sales ya yi bayanin ne a wani jawabi da ya yi wa manema labarai kan bayanan ma’aikatar harkokin wajen Amurka na shekarar 2017 akan ta’addanci wanda ya nuna cewa kungiyin ISIS da Alkaida sun kara bazuwa, kuma sun koma amfani da yanar gizo wajen ingiza magoya bayansu a wurare daban daban su kai hare-haren ta’addanci.

 

Advertisement

labarai