Kura-kuren Da Hukumomi Ke Yi Wajen Bayar Da Rance

Zamani

Daga Aliyu M. Kurfi (PhD),

Ya kamata mu sani cewa akwai wasu kura-kurai da hukumomi ke yi wajen bayar da rance, wadanda ke jawo durkushewar sana’oi a jihohinmu. Ga wasu daga ciki kamar haka:

 

Tsarin ‘Kwali Jari’

Wannan babi zai yi bita ne a kan wasu daga cikin abubuwan da wasikarmu dangane da KWALI JARI zuwa ga gwamnatin tarayya ta kunsa. Sai dai yana da kyau tun kafin a yi nisa mu sanar da maikaratu cewa abin da zai karanta dan tsakure ne daga wasikar, amma ba dukkanta ba, kuma a cikin harshen Turanci muka rubuta ta. Fatarmu dai ita ce, a fahimci cewa abin da za a karanta a babin ba dukkan abubuwan da wasikar tamu ta kumsa ba ne. Kafin dai mu aika wa gwamnatin tarayya wannan shawara tamu sai da muka gabatar da ita a kafafen sadarwa, wadanda suka hada da gidajen rediyo, da kafafen sadarwa na zamani, watau na yanar gizo, kai har tarukan jama’a mun kira, domin a tattauna wannan tsarin a wasu daga cikin jihohinmu na Arewa-maso-Yamma, wadanda suka hada da Katsina da Kaduna da Kano da Zamfara da Jigawa. Lokacin wannan zagaye namu na tuntuba, mun samu rakiyar wasu daga cikin ‘yan Kungiyar Muryar Talaka.

Mun amfana matuka daga shawarwarin da jama’a suka bayar. Yanzu ga wasu daga cikin batutuwan da muka ciro daga wasikar tamu ga gwamnati, dangane da tsari na KWALI JARI. Bismillah! ….

Wannan tsari da muka gabatar a nan, mun lakaba masa suna KWALI JARI. Babban abin da ake bukata a tsarin shi ne samar wa matasanmu rancen kudade domin su yi sana’a, ta hanyar karbar takardunsu na shaidar kammala babbar makaranta, a matsayin jingina.

 A yau, saboda rashin aikin yi wasu daga cikin matasan namu sun kasance ‘yan ta’adda, masu yin garkuwa da mutane, da kuma aikata sauran miyagun dabi’u. Muna da tabbacin cewa za a iya dawo da kimar takardun shaidar ilimi na kammala manyan makarantu ta hanyar yin amfani da wadannan takardu a matsayin jingina, domin bayar da rancen kudade ga matasanmu su yi jari. Saboda haka muna bayar da shawara a amince domin yin amfani da takardun shaidar kammala manyan makarantu, a madadin takardun mallakar fili ko gida wajen bayar da rance. A fili take cewa wannan lokaci da muke ciki, akwai matasanmu wadanda suka kammalla manyan makarantun jibge a birane da garuruwanmu, da a yau suke zaune ba tare da sanin me za su yi ba. Baya ga irin wadannan matasa da ke zaune babu abin yi, duk shekara kuma ana yaye dubbai daga manyan makarantunmu. 21 Sanin kowane cewa hanyoyin da aka dade ana bi wajen samawa matasa sana’oi, hanyoyine na wucin-gadi, wadanda ba masu dorewa ko tasirin kirki ba. Daya daga cikin irin wadannan hanyoyi shi ne Sure-P, da gwamnatin da ta shude ta samar, wanda kuwa mun sani ko a wancen lokacin kalilan ne daga matasan namu masu takardun shaidar kamalla manyan makarantu suka amfana da shi.

Manufar wannan tsari namu na KWALI JARI, shi ne ya taimaka wajen samarwa matasanmu rance kudade domin yin jari, ta hanyar karbar takardunsu na shaidar kammala manyan makarantu da na yin hidimar kasa a matsayin jingina. Mun fahimci cewa ita kanta gwamnati da bankuna za su iya taimakawa wajen magance wannan matsala. Hujjarmu ta Neman a yi Amfani da Wannan Tsari

Exit mobile version