Daga Mustapha Ibrahim, Kano
- An Koka Kan Abinci, Zirga-zirga Da Makwanci
- Mu Dai Yi Iyaka kokarinmu Fa, Cewar Masu Gudanarwa
Kamar dai yadda rahotanni suka gabata cewa, an gabatar da musubakar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 35 da aka gabatar a Birnin Kano kuma har jihohin Kano da Zamfara sun samu nasara, inda Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa gwarazan da suka samu nasara hidimar sha tara ta arziki, don karfafa gwiwar makarantan da sauransu.
Sai da kuma Wakilin LEADERSHIP A YAU ya yi naziri da bincike da kuma jin korafe-korafen mahalatar musabakar daga bangarori na masu ruwa da tsaki a musabakar da nufin yin gyara nan gaba.
Su kansu ’yan jarida masu dauka rahotannin musabaka da suka bukaci a sakaya sunansu sun bayyana yadda suka fuskanci karacin abinci a wannan musabaka ta Kano bisa la’akari da yadda suke samun abinci da walwala a sauran jihohin da suke halata duk shekara.
Wani daga cikin ’yan jarida da suka zo daga wata jiha ya ce, an ba su masauki a wani otel, amma na’urar sanyaya daki ba ta aiki, sai da suka kai gwauro suka kai mari sannan aka kawo musu wata fanka kodayake a kwanansu na karshe an gyara na’urar. Haka kuma motar zirga-zirga da aka ba su, an ce sau uku za a dauke su a kai su wurin da safe zuwa rana a dawo da su masauki su huta, kafin a koma da yamma, amma hakan ta gagara, sai dai akai su da safe wajen taro su yi ta zama har sai dare a zo a dauko su.
Haka su ma wasu jami’ai ko kuma malamai ’yan kwamitin na musabaka daga wasu jihohin kasar sun koka da karancin masauki da abinci har da karancin ruwan sha. Shi ma haka wani ya ce, “a jihohi irin su Edo, Lagos da sauransu, ruwan roba ya wadata ko da wanka ka ke so ka yi da shi, sakamakon gudunmowar al’ummar jihohin da gwamnatocinsu, amma banda a Kano wannan karon.”
Kan wannan korafi na bakin musabakar kasa a Kano ya sa Wakilinmu ya ji ta bakin shugabannin kwamittin karbar bakin taron na Kano, Sheikh Ibrahim Shehu Mai-Hula, inda ya ce, ya samu wannan korafi, amma matsalar ita ce yadda kwamittin tsara musabaka na kasa da yake Sakkwato ya tsara adadin mutane masu zuwa taron su ne, Kano ta san da zamansu kawai kuma su ta yi wa tanadi, amma wasu na kara adadin da babu su a rubuce.
Ya ce, “misali a ka’ida mutum 15 ne wata jahar za su zo, sai su zo da mutum 30, wai don shirin ko-ta-kwana, alhali tsarin na mutum 15 ne kuma.”
Ya kara da cewa, “duk jihar da ta kara, ita za ta dauki nauyin kanta, kamar yadda mu nan Kano idan mun kara zuwa wata jihar mu ne muke daukar nauyin kanmu.”
Shi kuwa Gwani Yahuza Gwani danzarga, Mataimakin Shugaban Kwamitin Karbar Bakuncin Musabakar a Kano, ya ce, “duk wanda ya yi korafin karancin abinci ko masauki makaryaci ne, domin duk ’yan takara da ’yan kwamiti an san adadinsu, kuma an ba su komai na masauki da abinci ba tare da wata matsala ba.”
Shi ma Alhaji Mustapha Mai Nasara kofar Nassarawa, Shugaban kungiyar ’Yan Jaridu Masu Bada Labaran Mussabaka na kasa, a tsokacinsa ko martaninsa, ya ce, “Kano ta yi cawar gani gurin ba da masauki da abinda ya kamata, amma dai kowa ya san wannan lokaci sai hakuri, saboda yanayin karayar tattalin arziki sakamakon zuwan annobar ciwon Korona. Amma duk ’yan jaridu an ba su masauki da abinci da kuma abin hasafi, kamar yadda ake ba wa irin masu wannan aiki na musamman, indai daga wata jahar ya zo tunda dai ni ne shugaban kungiyarsu na kasa.”
Idan aka koma batun tofa albarkacin baki kan ita kanta musabakar, masu ruwa da tsaki sun tofa albakacin bakinsu.
Alhaji Nuhu Gudaji shi ne Sakataran Yada labarai na wannan Kwamiti na Musabaka. Ya ce, “Kano ce kan gaba wajan samun nasarar gwarazan musabaka a Nijeriya tunda aka fara a 1986, inda Marigayi Gwani Aminu Zaina da Marigayi Malam Ja’afar Mahmud Adam da irinsu Gwani Kabiru suka wakilci Nijeriya. Kusan sau 16 Kano na samun nasara a matakin kasa da wakiltar Nijeriya a gasar karatun Alkur’ani mai girma.”
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano da Arewacin Nijeriyam Sheikh Ibrahim Khalil, kuwa ya bukaci dalibai su dage da karatu, wanda a cewarsa, hakan shi ne ma’anar yin musabakar.
Shi kuwa Alhaji Yusif Abdullahi, Mataimakin Shugaban Kwamitin Musubaka ta Zamfara, ya ce, “su a matakin jiha ma na musabaka Gwarzo da Gwarzuwa, an ba su motoci da kujerun Makka da sauran kyatutuka daga Gwamnatin Muhammad Bello Matawalle da sauran jama’ar Jihar Zamfara.”
To, a Kano ma an shin ina kyatutukan Kanawa ga Gwarazan? Ko sai Gwamnan Kano kawai ya ba Gwarazan kyauta?
A nasu bangaren, wasu daga cikin manyan ’yan kasuwa a Kano irin su mai kamfanin BUA, wato Alhaji Abdulsamadu Shiekh Isyaka Rabiu, wanda Gwani Lijan da Alhaji karami suka wakilta, ya ba wa ’yan kwamitin musabakar kyauta Naira million 10. Alhaji karimi Isyaka Rabiu kuma ya ba su Naira miliyan biyu, sai Alhaji Aminu dantata ya bada Naira miliyan 10.
Wadannan duk kwamitin musabaka suka ba wa kyautarsu. Sai dai kuma Alhaji Muhamud Gwani daga Jos ya bayar da Naira miliyan 20 ga daukacin wadanda suka samu nasara a kowane mataki na gasar karatun maza da mata a musabakar ta 35 da aka yi a Jami’ar Bayero ta Kano. Sai kuma kyaututtukan atamfa daga Alhaji Sabiu Bako da Alhaji Tukur Gadanya da sauran wasu ’yan kasuwar Kano, an dai fara musabakar ne a ranar 19 ga watan 3 zuwa 27 ga watan na shekara ta 2021.
A karshe Wakilin LEADERSHIP A YAU ya rawaito mana cewa, jama’a da dama sun koka kan rashin manyan jami’an gwamnatin Kano da suke halartar taron musabaka a kowacce rana, inda hatta ranar Juma’a, wato jajiberin bikin fidda gwarazan ba a keyar da yawansu ba.