Kurdawan Iraki sun gudanar da kuri’ar raba gardama ta ballewa daga kasar domin samun ‘yancin kai a ranar Litinin da ta Gabata. Kurdawan sun bijerewa dukkanin wata barazana da gargadi daga Iraki da Iran da kuma Turkiya da ke adawa da matakin gudanar da kuri’ar.
Dubban Kurdawa ne suka jefa kuri’ar da za ta ba su damar ballewa daga Iraki domin samun ‘yancin gashin kai.
Kurdawan sun yi shiga sanye da tutarsu mai launin ja da fari da kore da kuma doruwa tare da kawata unguwanni da tutar a sassan arewacin Iraki da suke fatar samun ‘yanci.
Kurdawan sun jefa kuri’ar duk da gargadi daga gwamnatin Iraki da kuma barazanar takunkumi daga Turkiya da Iran da ke makwabta da su.
Tuni dai Turkiya ta ce za ta rufe kan iyakarta da yankin na Kurdawa tare da hana su fitar da mai.
Kabilar Kurdawa ne na hudu a yawan jama’a a yankin gabas ta tsakiya kuma har yanzu ba su da wata kasa mai cin gashin kanta.