A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin.
A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya.
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince cewa, baje kolin CAEXPO ya bayyana yadda Sin da kungiyar ASEAN suka himmatu wajen bunkasa bude kofa bisa matsayin koli, da kare tsarin cinikayya cikin ’yanci da kasancewar mabambantan sassa.
Kafar CGTN ta gabatar da kuri’ar ne da harsunan Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da yaren Rasha, inda kuma mutane 6,260 suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’ao’i 24. (Saminu Alhassan)