A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba.
An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken CGTN, kashi 71.5 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun ce takarar dake tsakanin jam’iyyu biyu na kasar ta tsananta matsalolin zamantakewar al’ummar kasar, kashi 74.4 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyi sun ce takarar dake tsakanin jam’iyyun biyu ta shaida rikici da matsaloli kan tsarin siyasa na kasar Amurka, kuma kashi 73.2 cikin dari suka ce ana bukatar yin kwaskwarima kan tsarin siyasa na kasar ta Amurka. (Zainab Zhang)