Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: Masu Bayyana Ra’ayi Sun Zargi USADA Da Yin Rufa-rufa
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: Masu Bayyana Ra’ayi Sun Zargi USADA Da Yin Rufa-rufa

bySulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Cgtn

Batun rufa-rufa game da dan wasan tseren Amurka Erriyon Knighton da aka zarga da amfani da abubuwa masu kara kuzari yayin wasa, ya bankado zargin da ake yiwa hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari yayin wasanni ta Amurka wato USADA da boye gaskiya, da yin fuska biyu, da amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba.

Game da hakan, wasu kuri’un al’umma da kafar CGTN ta tattara sun nuna kaso 95.57 bisa dari na al’ummun da suka bayyana ra’ayoyinsu daga sassa daban daban na duniya, na zargin USADA da yiwuwar rufe gaskiya kan ’yan wasan Amurka, da aka tabbatar sun yi amfani da abubuwa masu kara kuzari.

  • Hukumar Yaki Da Shan Maganin Kara Kuzari Yayin Wasanni Ta Duniya Ta Fallasa Ayyukan Amurka Game Da ’Yan Wasa Masu Keta Ka’idoji
  • Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Karshen Matsin Rayuwa – Gwamnan Bauchi 

A watan Maris da ya shude, hukumar yaki da amfani da abubuwa masu kara kuzari yayin wasanni ta kasa da kasa WADA, ta samu Erriyon Knighton da laifin amfani da abubuwan kara kuzari, amma duk da haka hukumar USADA ta kyale shi ya shiga wasu wasanni ba tare da la’akari da hukuncin WADA ba. Sai dai kawai USADA ta ce wai dan wasan ya ci wani nama ne gurbataccen wanda ya sanya aka same shi da wancan laifi.

Amma a daya bangaren WADA ta fitar da sanarwa, inda ta ce ba ta taba baiwa hukumar USADA ikon barin irin wadannan ’yan wasa da aka kama da lafin su shiga gasanni ba, domin hakan zai iya zubar da kimar gasanni.

Game da hakan, sakamakon kuri’un jin ra’ayi na CGTN, sun nuna cewa kaso 90.15 na jama’ar da suka bayyana matsayar su na ganin Amurka ta rufe laifin Knighton, har ta ba shi damar shiga gasar Olympic ta birnin Paris, wanda hakan ya yi matukar gurgunta kima da makasudin gasanni. Har ila yau, kaso 96.54 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na ganin abun da Amurka ta yi misali ne na yin fuska biyu. Yayin da wani kason da ya kai 95.63 bisa dari ke ganin da yawa daga yan wasan Amurka na gabatar da shaidun bogi na gwaje gwajen da aka yi musu.

Bugu da kari akwai kaso mai yawa da ya kai 96.23 bisa dari dake ganin ya dace a kara yawan gwajin da ake yiwa ’yan wasan Amurka masu halartar gasar Olympic ta Paris, domin dawo da kima da kwarin gwiwar adalci tsakanin sassan kasa da kasa kan gasar.

An gudanar da kuri’un jin ra’ayin al’ummar na CGTN ne ta harsunan Turanci da Faransanci, da Larabci, da harsunan Sifaniya da Rasha, inda masu bayyana ra’ayi 14,580 suka fayyace matsayarsu cikin sa’o’i 16.
(Mai Fassara: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Daga Birnin Sin

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Next Post
Kasar Sin Ta Yi Karar EU A WTO Kan Matakan Wucin Gadi Kan Motocin Lantarki Na Kasar Sin

Kasar Sin Ta Yi Karar EU A WTO Kan Matakan Wucin Gadi Kan Motocin Lantarki Na Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version