Dokta Aliyu Ibrahim Kankara">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTAUNAWA

Kuruciya Ta Sanya Ni Yawo Ba Rashin Galihu Ba —Lami Shagamu

by Dokta Aliyu Ibrahim Kankara
September 8, 2019
in TATTAUNAWA
10 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A kwanakin baya ne, ranar Alhamis, 29/8/2019 shaharraen marubuncinmu kuma Malami a jami’ar tarayya ta Dutsinma dake jihar Katsina, Dokta Aliyu Ibrahim Kankara ya ziyarci Hajiya Lami Iyabo, wadda aka fi sani da Lami Shagamu a gidan ta da ke Kano ya zanta da ita a kan rayuwar ta da, al’amurran rayuwa da suka shafe ta. Ga yadda hirar su ta kasance: 

Hajiya, a cikin shekarar 2013 a watan Fabrairu ina a gidan Telbijin na Jihar Bauchi ana yin hira da ni ta ‘kai tsaye’ na bugo ma ki waya kin dauka mun yi magana, don wani ne ya bugo waya yana tambayar tarihin ki, ya kuma nemi ya ji ko kina a raye? Shi ne ma na bugo ma ki don ya tabbatas kina a raye. Kin tuna lokacin?

E kwarai,na tuna lokacin, na kuma gode, Allah Ya saka maku da alkhairi.

To yanzu ma mun dai sake dawowa, kin san wanda duk Shata ya yi ma waka, to har abada ba za a daina tuntuba a game da shi ba. Kuma musammam, a yanzu da hanyoyin sadarwa suka yawaita, ana so a ji lallai kina nan a raye koko, duk dad a cewa ga littattafai nan an wallafa akan Shatan. Jama’a masoya wakokin Shata sun fi samun saukin duba bayanai nay au da kullum daga waya akan duba littafi. Don haka za mu so mu sake yin bita a kan tarihin rayuwar ki.

Ai kwarjinin Shatan ne ya shafe ki. In dai za a manta da Shata a Duniya, to kuma da ya wake za a daina batun ku.

Toh, Bismillahirrahmanir Rahim. Sunana Halimatu, amma da yake ran Alhamis aka haife ni sai aka boye sunana ana kira na da sunan rana. Nice diya ta fari a wajen mahaifin mu. Ana kuma kira na Iyami ko Iyabo saboda sunan mahaifiyar maigidan mu aka sanya ma ni.

Mahaifin ki mutumin Kano ne ko Shagamu? Muna so mu ji asalin iyayen ki.

Mahaifina mutumin wani kauye ne da ake kira Rigafada a cikin yankin Kumbotso. Shi manomi ne, kuma bai taba zama Kano ba. Sunansa Adamu Abdullahi. Mahaifiyata mutumniyar wani kauye ce da ake kira Kankare a yankin Sumaila ta jihar Kano. Sunan ta Madina, kuma sunan mahaifinta Malam Isiyaku. Kuma, akwai wani fitaccen mutum a Rijiyar Lemu da ake kira Alhaji Sabo Dan Canji, to kanen mahaifiyata ne. To ka san iyaye a da, suna tafiya fatauci daga gida. Wata rana, kamar yanda magabatana suka ba ni labari, mahaifin babata yana yawon karatu na addinin musulunci sai ya sauka Katsina. Sai Sarkin Katsina Usman Nagogo ya yanka masa haraba a kasar Katsina, inda ya kaishi shi ne Wawarkaza ta kasar Kankara. Har yanzu zuriyar mu na nan, ‘ya’ya da jikoki suna nan zaune a wurin.

Wato ke nan kin tashi a Rigafada ta yankin Kumbotso?

‘A’a, ba nan na tashi ba. Yadda abin yake shi ne, yayar mahaifi n ace ta ke zaune a Legas. Sai wata shekara ta zo gida daga can, sai ta tarar an haife ni. To sai ta dauke ni a matsayin riko, na bi ta can Ikko.

Yaya sunan ta ?

To kin tashi a Legas, yaya zancen karatun boko ko na Muhammadiyya?

Na yi makarantar Malam Liman a Agege, na kuma yi karatun Islamiyya da makarantar allo a unguwar Kwakwa uku, wadda ake kira makarantar Malam mai dan hanci. Amma ban yi makarantar boko ba, saidai na yi karatun yaki da jahilci a Agege, wanda ake zuwa da maraice (Ebening classes) Ka san ita Ikko, Yarabawa sun taushe komi, basu son Hausawa su amfana da wani abu wanda za a ce mai amfani ne a rayuwa. Ko a makarantun su na boko, za ka ga suna kyamar ‘ya’yan Hausawa. To wannan ta sanya Hajiya Kanti ba ta sanya ni boko ba.

A ina kuka fara haduwa da Dokta Shata har ya yi ma ki waka?

 

Gidanmu a Agege na kusa da gidan Alhaji Na’Allah Dan Ibrahim, wanda Shata ya yi ma waka. To duk sa’adda ya sauka Ikko sai Na’Allah ya kai shi a gidansa na saukar da baki a filin goro, a nan Agege. Akwai wata diyar Alhaji Na’Allah da ake kira Saude, kawata ce, ba mu rabuwa. To ni da ita ake ba abinci mu kai ma Shata a masauki. Wannan ke nan.

Sai aka yi mani aure a Legas. Amma sai na nuna ba na son mijin,na fara guje-guje.  Sai dole aka raba auren. To sai Hajiya Kanti ta ce tunda na ki zaman aure ba za ta zauna da ni ba, ta sallame ni na komo gida wajen iyaye na. To ka san Legas yadda ta ke, muddin kana zaune kudu, ba za ka iya zaman arewa ba. Sai na hau mota na koma Legas, ba tare da sanin iyaye na ba. Sai na tafi gidan Alhaji Salmanu a Agege, wanda shi ne mahaifin kawa ta, Hajara. Na nemi ya ba ni daki a gidan sa in zauna. Lokacin Hajara ‘yarsa ta yi aure. Sai ya ce ma ni ‘in ba ki daki a gidana ki zauna? Ai kamar na ba Hajara ne’. Ma’ana: yana nufin ba za ya ba ni daki in zauna a gidan sa ba tunda na ki zaman aure, tunda ya dauke ni kamar uba.

A daidai lokacin Salmanu na zaune suna hira tare da wani babban abokin sa, wani Bayarabe. Sai wannan Bayarabe ya ja ni ya kai ni wani sabon gidan sinima da aka gina, ana kiran sa Danjuma sinima, akwai dakuna sabbi da aka gina a ciki da ba a bai wa kowa ba. To shi ke kula da wurin. Sai ya tambaye ni, zan iya zama nan,  ga daki, kuma kyauta? Na ce masa ‘e’. Mafarin zama ne na biyu kenan a Legas, kuma a wannan sinima. Shikenan, in shiga can, in fada in, ina ta yin sabbin kawaye da samari.

Wanne Salmanu Agege ki ke magana? Ko Salmanu da na sani mutumin Zariya, shugaban ‘yan Daudun Afirka kwata?

E shi, ashe ka san shi.

Na san shi a cikin 1994 lokacin da na je Bautar Kasa (NYSC) a Ikko. Ai gidansa na je a Agege, na tambaye shi gidan Alhaji Na’Allah din, wanda ki ke magana. Na’Allah na da Awwalu?

E, kwarai, akwai Awwalu a cikin ‘ya’yan sa.

To Kankara, ka san yaro da shirme, ni hankali na ko kusa bai tafi ga Shata ba, ballantana in yi tunanin inyi kwadayin ya yi ma ni waka. A daidai lokacin muna kokarin mu gudu daga wajen su daddy Salmanu mu tafi daji, akwai gasa ta shan ‘maro’ da samarin Shagamu suka shirya, a tsakanin su da mu, mu baki da muka je daga Legas. Ana so a yi gasar (competition) a ga su wa suka fi shan maro.

Minene maro? Ko ita ce ‘marijuana ko wiwi?

E, kwarai ita ce.

Yawwa Hajiya, ina jin ki.

Mun taba haduwa a gidan san a BCGA a Funtuwa. Motar mu ta lalace a Funtuwa, kuma a daidai gidan. Sai nace ma wata kawata ta zo ta raka ni wajen wata kawarmu kuma wadda ke zaune a wannan gidan na Shata. Da muka hau bisa bene muka same ta a daki, muka gaisa, sai ta ce mu je kasan bene, Baba na nan mu gaishe shi. Na ce mata wane Baba kuma? Ta ce ‘Shata’. Muna sauka kasa muka tarar da shi. Yana gani na sai ya ce ‘Lami, na samu kudi ba kanana ba da wakar ki, wakar ki ta kara mani farin jini ma’.

Hajiya, bayan Legas, kin zauna wani gari koko? Ko nan Legas kadai ki ke da wayau?

Uhmmm, Kankara kenan. Kai, bari ka ji in fada maka, ni fa na zauna gidan Fela Aniukulapo Kuti, kanen Ransom Kuti. Na yi masa waka. Bayan ma ni, ni na kai masa wata kawaye na an ace masu A’isha Maiduguri. Da wata Fati. Ita Fatin ma tare muka zauna Katsina. Har yanzu Fati tana nan Gabi Hotel. Katsina, mai wurin ma har ya ‘yanta ta, zaune take kyauta ba ta biyan kudin haya. Ita ta ki yin ritaya daga yawo.

Uhhmmm, Fela mai waka?

E, shi mana. Na san Fela tun yana koyon waka. Tun baya da ko kwabo, tun yana zuwa koyon waka a gidan kwano-da-kwano. Yana zama yana kada ‘yar jitar sa shi kadai, tun bai ma san za ya tara wadannan matan ba. Mu kuma a lokacin muna ‘yan yara kanana muna zuwa kallon sa. Sai mu rika leken sa ta kafar hudar kwano, muna kallon sa ana korar mu. Har sai da ta kai na yi zama wajensa lokacin da ya rika ya zama abin tsoro. Wakokinsa na ‘Oh, jarajo, zombi’ duk muna tare ya yi su.

Lallai, ashe dai Hajiya, an sha Duniya, an dangane, an kure mizanin yawo, tunda har an zauna gidan Fela.

Har Katsinar taku sai da na zauna. Na zauna a gidan wani Dan Daudu da ake kira Alhaji Bello Bala’i, mutumin Gusau, a nan bayan tasha. Lokacin da aka bada jiha cikin 1987 ai duk lokacin ina Katsina. Ka san wadda ake kira Lamin Bole a Katsina? A’a, Hajiya.

To nice. Saboda saurayina wadda mu ke tare da shi da ake kira Ibrahim Bole. Amma ya rasu tuni.

E, kwarai, nima ina jin sunan Bole amma ban taba ganin sa ba. To bayan wannan zamani, an yi wani auren koko?

Kwarai, na yi aure-aure bayan na komo Kano da zama. Amma Allah Bai sanya aurarrakin sun dore ba. Wannan mijin nawu na baya da muka rabu, nan gidan muka zauna da shi, amma gida na ne.

Kin taba haihuwa? A cikin matan da Shata ya wake wacce ki ka sani, kuma da wacce ku ka zauna tare?

E, ina da diya daya da na haifa da mijin baya, sunan ta Hassana. Ita kan ta sai da ta yi girma har ta yi aure ta haihu. Haihuwar ta uku, amma yanzu ta rasu. ‘Yayan na can wajen ubansu. A halin yanzu ba ni da da ko daya saidai wadannan jikoki.

A cikin matan da Shata ya wake, na san Hajiya Hauwa mai tuwo, muna gaisawa da ita. Daga nan kuma na san Goshin Dangude, don har ma mun taba zama tare a Zariya.

Allahu Akbar Khabiran, Allah Ya jikan ta, Ya raya mata abin da ta bari. To yanzu mi ki ke yi, kina sana’a?

E, kwarai, ina yin siyasa. Duk fadi-tashin da aka yi da gwamnatin Kwankwaso da mu aka yi. Mu muka sha wahalar waccan gwamnatin, amma har yau din nan ba a saka mana ba. Har gida na na sayar, banda wannan, na bayar da kudin aka yi kamfe, saboda nice shugabar mata (women leader) Da gwamnatin Kwankwaso ta zo karshe, sai ya tara mu, ya ba mu hakuri, ya ce ya san cewa ba a yi mana komi ba, amma ga sabuwar gwamnati ta Ganduje, mu bi ta. Ya ma hada mu da shi. Mun sake sadaukar da rayuwar mu mun bi ta, daga baya kuma suka bata. Yanzu ba mu ga tsuntsu ba mu ga tarko. Duk mun bata lokutan mu ga gwamnatocin biyu a banza, mun sayar da duk kaddarorin mu, ba sakayyar da aka yi mana. Sai wasu sabbin zubi, ‘yan adawa ma, da aka lallaso suka shigo kwanan nan, su ke cin gajiyar wannan sabuwar tafiyar. Abin sai dai addu’a, Allah Ya kawo mana mafita don iyyaka na’budu.

Allah Za ya kawo fatahi a gaba insha Allahu. Hajiya, na gode, na bar ki lafiya.

Amin Dokta Kankara, na gode. Allah Ya mayar da kai gida lafiya.

Kankara: Amin Hajiya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Da Sana’ar Gyara Takalmi Na Sayi Gida –Adamu Shoe Shiner

Next Post

Me Yasa ‘Yan Afrika Ta Kudu Suka Tsani Bakin Haure?

RelatedPosts

Har Yanzu Babu Sabuwar Kwalta Ko Kwalbati A Garin Giwa – Kwamred Alkurkawee

Har Yanzu Babu Sabuwar Kwalta Ko Kwalbati A Garin Giwa – Kwamred Alkurkawee

by Dokta Aliyu Ibrahim Kankara
1 week ago
0

Daga Idris Umar Game da more romon dimukradiyya da wasu...

Zaman Lafiya

Marasa Son Tabbatuwar Zaman Lafiya A Nijeriya Ke Sukar Furucin Gwamna Bala Kan Fulani, Inji Ladan Salihu

by Dokta Aliyu Ibrahim Kankara
2 weeks ago
0

DAKTA LADAN SALIHU Shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar...

Giratuti

Mun Samar Da Daftarin Cigaba Na Shekara 10 Ne Domin Kafa Harsashin Inganta Rayuwar Gombawa –Gwamna Inuwa

by Dokta Aliyu Ibrahim Kankara
2 weeks ago
0

ALHAJI MUHAMMAD INUWA YAHAYA Shine gwamnan jihar Gombe, a wani hira ...

Next Post

Me Yasa ‘Yan Afrika Ta Kudu Suka Tsani Bakin Haure?

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version