Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTAUNAWA

An Kusa Kawo Karshen Barace-barace A kasar Nan —Goni Sheikh Musa

by Tayo Adelaja
September 11, 2017
in TATTAUNAWA
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Goni Sheikh Hassan Musa Minna Shi ne shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani ta Kasa, limamin da ke gudanar tafsiri a gidan tsohon shugana kasa Janar Babangida, gwani a harkar Alkur’ani kuma marubuci. Ya bayyana wa wakilinmu Abdullahi Mohammed Sheka yadda Ahlullahi ke alfahari da gudunmawar da mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayar wajen hada kan al’ummar musulmi, sannan kuma ya yi tsokaci kan yadda dalilin mai alfarmar mahaddata a yau ke cikin sahun wadanda ake tattaunawa da su kan abubuwawan da suka shafi harkokin addinin Islam da ci gaban kasa. Sai kuma shirin wannan Majalisa domin tabbatar da ganin matsalar barace-barace ta zama tarihi a kasarnan. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Wane hali shirin majalisar Mahaddata alkur’ani ta Kasa ke ciki na kawo Karshen barace baracen da aka jima ana tattaunawa?

samndaads

Alhamdulillahi muna yi wa Allah godiya da Ya ba mu ikon yi wa hakar Tsangayu kallon tsanaki, musamman kasancewar dukkanmu cikin wannan tsari muka taso har kuma Allah cikin jin KanSa ya kawo mu halin da muke ciki a yanzu. Mun jima muna gudanar da bincike tare da tuntubar masu ruwa da tsaki a cikin harkar karatunmu na tsangaya, kuma alhamdulillahi kwalliya na biyan kudin sabulu, musamman idan aka dubi yadda ’yan’uwa alarammomi suka karbi wannan shiri, wanda shi ne irinsa na farko da zallar alarammomi na hakika ba alarammomin mota da ofis ba suka runguma, wannan kuwa ya biyo bayan irin gudunmawar da mai alfarma Sarkin Musulmi Dakta Sa’ad Abubakar III yake badawa ne.

Batun bara kamar yadda na sha fada abu ne da aka yi wa dibar karan mahaukaciya shekaru masu yawa da suka shude, amma sai yanzu ne a karkashin shirin wannan majalisa muka tashi tsaye domin hada kan alarammomi, gardawa, titibirai da kuma kolawa. Muna yin duk mai yiwu a halin yanzu domin tabbatar da kididdigar  yawan makarantun allo, tsangayu, yawan almajiran da ke kowacce tsangaya tare da malamansu. Sai kuma yin nazari tare da samar da hanyar sanin zirga-zirgar alamajirai daga wannan gari zuwa waccan ko daga waccan kasa zuwa waccan.

 

Goni kamar yadda ka ambata irin gudunmawar da ka ce mai alfarma na yi wa  harkokin Alkur’ani, shin iya haka ya tsaya ko akwai sauran tagomashin da al’ummar musulmi ke amfana, musamman ganin yanzu ya zarta shekara goma a kan karagar Sultan a wannan kasa?

Alhamadulillahi idan ka duba ko in ce ka waiwaya baya shekaru goman da mai alfarma ya yi a kan wannan kujera mai albarka, ba musulmi kadai ba har  wanda ba musulmin ba ma ya amfana da jagaorancinsa. Da farko dai sama da shekara 30 aka shafe ba a taba samun watan Ramadan da al’ummar musulmi suka tashi da azumi baki daya ba sai a shekararsa ta farko da hawa wannan kujera, kuma tun daga wannan lokaci ake kara samun daidaito a harkar  dauka da sauke azumin watan Ramadan.

Na biyu kuma, mai alfarma ya samar da dandamalin da ke zaman allurar  dinke mafi yawan sabanin da ya jima yana addabar al’ummar musulmi, wannan kowa zai gasgata maganata idan ka duba wata kungiyar shugabannin kungiyoyin addinin musulunci na Arewacin Nijeriya, wanda a halin yanzu ake gudanar da taruka ana zama wuri guda, ga ‘yan Izala ga shugabannin Darikun Tijjaniyya da Kadiriyya, ga kungiyoyin mata da kungiyoyin dalibai musulmi, a ci tare a sha tare, a kwana a wuri guda ana tattauna wasu abubuwan da ake fatan kamo bakin zarensu. Wannan ba karamar  nasara aka samu ba.

 

Kamar yadda ka fara ambatawa tuni wannan majalisa ta yi nisa wajen binciko hanyoyin kawar da barace-barace, wane haske kuka fara gani da ke tabbatar da nasarar wannan shiri?

Ina tabbatar maka da cewar yanzu haka akwai wasu hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da wajen kasar nan. Alal misali, akwai wata kungiya da ake kira MAFITA tuni muka shigar da wasu tsangayu da aka fara gwajin koyar da ilimin zamani da kuma sana’o’i musamman a Jihar Kano wanda insha Allah sama da almajrai dubu ashirin ake sa ran koya wa sana’o’i iri daban-daban.

Bayan haka, mun fara gwajin hana almajirai bara a wasu tsangayu ta hanyar koyar da kolawa sana’o’in da za su dogara da kansu. Sannan muna da tsarin kiwon lafiya a matakin farko, wanda muke gayyatar masana harkar lafiya domin bayar da horo na wasu ‘yan kwanaki, wanda dalibanmu za su san matakan bayar da taimakon farko a duk lokcin da bukatar hakan ta taso, hakan na haifar mana da ci gaban da ake bukata. Saboda haka, muna da kyakkyawan zaton idan hukumomin suka ba mu hadin kai tare da tallafa wa wannan majalisa ko shakka babu a cikin shekara uku da yardar Allah abubuwa za su sauya.

 

Babban abin da ake ta korafi a kan harkar almajirci bayan bara akwai matsalar rashin tsafta, shin Majalisarka kun dubi wannan bangaren kuwa?

Alhamdulillahi wannan matsala ita muka fara dubawa, tare da yin nazarin abin da ke haifar da ita, mun fahimci rashin isasshen wurin kwana, abinci mai gina jiki da wuraren zagayawa su ne ke haifar da wannan matsala. Kuma mun fahimci rashin mayar da hankalin iyayen yaran da ke tura ‘ya’yansu neman ilimin Alkur’ani, shi ke zaman kadangaren bakin tulu ta wannan fuska. Saboda haka yanzu haka, muna gudanar da shirin fito da wani tsari na iyaye su ci gaba da daukar nauyin abinci, wurin kwana da sabulun wanka da na wanki. Idan wannan tsari ya fara tabbata za mu tabbatar kafin a karbi yaro sai an tabbatar da ingancin wurin kwanansa da abincinsa. Idan aka samu wannan damar su kuma alarammomin su ne muke fatan samar musu da sana’0’in da za su dogara da su a wuraren da tsangayun suke, suna gudanar da dan kasuwanci, noma ko kiwo. Hakan zai bai wa alaramma damar samun sukuni da nutsuwar koyar da almajiransa.

A halin yanzu shi ma wannan shiri akwai tsangayun da muka fara gudanar da gwajin wannan tsari, kuma muna fatan insha Allah za a samu dacewa.  Wannan ta sa muke son hukumomin lafiya su ba mu hadin kai domin ganin harkar lafiya ta zauna daram a tsangayunmu.

 

Yanzu haka  da mai alfarma ke cika shekara goma a kan wannan jagoranci na al’ummar musulmin kasar nan, kasancewar wannan majalisa na cikin wadanda suka shaida irin alfanun jagorancin na sarkin musulmin, shin ko wane shiri mahaddata Alkur’ani suka yi domin bada tasu gudunmawar  wajen tabbatar da taron ya samu nasara?

Alhamdulillahi wani ma ya yi rawa balle dan makada, ai idan ana biki a gidan farar kaza  ba sai an gayyaci balbela ba, mahaddata Alkur’ani sun shirya taron addu’o’i da kuma taron kara wa juna sani domin ganin wannan taro an  yi shi lafiya an gama lafiya, sannan kuma mahaddata a duk inda suke mun bayar da umarnin gudanar da addu’o’i domin Allah ya kara wa shugaban kasa lafiya da mai alfarma sarkin Muslmi da sauran shugabanninmu.

 

Wane fata wannan majalisa da kake shugabanta ke da shi nan gaba?

Fatanmu shi ne a samar da tsarin da makaratun tsangaya domin su ci gaba da amfana daga arzikin kasa kamar yadda sashin ilimin boko ke amfana. Haka kuma muna kira ga gwamnatocinmu musamman wadanda suke da tsarin tura dalibai zuwa kasashen waje  karo ilimi su shigar da alarammomi, kasancewar a kasashen da suka ci gaba akwai masu irin wannan ilimin a kowanne fanni kuma ana damawa da su. Haka batun daukar ayyukan gwamnati da sauran kamfanoni a bayar da dama ga alarammomi domin shiga cikin tsarin, yin hakan zai taimaka wa kokarin wannan majalisa na kakkabe hakar barace-barace  a kasarnan baki daya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Yaron Da Kishiyar Mahaifiyarsa Ta Yankewa Al’aura Ya Rasu

Next Post

Burinmu Tallafawa Mata Da Kananan Yara —Hajiya Murjanatu

RelatedPosts

Shugaban RIFAN

Kowa Ya Ci Bashin Noma Sai Ya Biya – Shugaban RIFAN Na Kano   

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa na Kasa  (RIFAN) reshen Jihar Kano,...

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

HON. MUHAMMAD UBA GURJIYA MAI SHANU shine wakilin al'ummar karamar...

Gwamnatin Jihar Kano Tana Bukatar Kowa, Inji Ibrahim Usman Bala

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Haruna Akarada, A ci gaban da gwamnatoci ke kokarin...

Next Post

Burinmu Tallafawa Mata Da Kananan Yara —Hajiya Murjanatu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version