Yasir Ramadan Gwale yasirramadangwale@gmail.com +23408099272908
Idan mutum ya kalli rayuwar ‘yan Arewa ta fuskar siyasa da tattalin arziki da habakar al’umma da cin moriyar abubuwan da zamani ya zo da su, sai ya ga cewa kullum fintinkau ake yiwa ‘yan Arewa. Sau da dama mukan yi kuskuren daukar layi daya domin tafiya akansa akan kowanne fanni na rayuwa kama daga abin da ya shafi siyasa da tattalin arziki da sauransu. Da yawa suna ganin dan mu mutanan kirki ne, mun karanta addini, mun fahimta, sai gaba dayanmu mu zama uztazai masu wa’azi, duk wanda ka gani daga cikinmu wa’azi yake saboda ya karanci addini, daga bisani kuma wadanda ake yiwa wa’azi su yita kokarin shigar da hassada da kiyayya da gaba a tsakanin Malamai masu wa’azi. Duk wanda yake jin ya karanta ilimin addini burinsa yazo ya samu masallaci da makaranta ya tara jama’a yana wa’azi, bama tunanin samar da wani abu sabo da zai taimakawa al’ummarmu.
Haka kuma, idan muka duba fannin kasuwanci, musamman irin na zamani, da yawan ‘yan Arewa mukan yi kuskuren raja’a akan abu daya. Duk wata harka ta kasuwanci da akaga tana garawa sai duk jama’a a hadu a yi mata rubdugu sai an ga an kureta ta zama babu riba, da kyar kudi suke dawowa, sai a sauya layi.Idan ka dauki harkar otal-otal haka ‘yan Arewa suka hadu suka kashe sana’ar otal, har ta kai yanzu ‘yan Arewa ba zasu iya bugar kirji da sana’ar otal ba, duk da cewa da dama sun yiwa otal muguwar fahimta.
Kasuwancin zamani irinsu harkar kayan masarufi da ake yi a manyan kantuna, da akaga tana garawa, yanzu kowane mutum ya ga ya dan samu kudi sai ya gina katafaren gini ya bude katon kantin kayan kamfani.Itama harkar gidan abinci haka ake yi mata.Harkar sayar da kayan sadarwa da suka ha]a da wayar salula da dangoginta haka abin yake, duk wannan yana faruwa ne, kuma bayan hassada da bakinciki da cin dunduniya da ake yiwa juna a harkar kasuwancin.
Yanzu, kusan mafiya yawan harkokin kasuwancin zamani da ake samun mawaliti, duk sun zama babu wata riba ta kuzo mu gani, an hadu an kurewa komai maleji. Itama harkar kayan sawa da kayan mata da ake zuwa Dubai da Cana a saro a zo a sayar duk sun zama babu wata riba mai gwabi kamar yadda ake yi a baya. Ka dauki duk wata harka za ka ga haka ake yi mata. Harkar gidan mai (Filling Station), ‘trabel Agency’, Gidan Gona da sauransu duk haka aka rusa su, suka zama babu wata riba mai ma’ana. Ba laifi bane a samu mutane da yawa a dukkan harkokin rayuwa na abubuwan bukatar yau da kullum duba da irin yadda jama’a ke karuwa cikin sauri, kuma bukatun na karuwa, amma ya zama muna yin komai da tsari da manufa, wannan shi ne zai sanya mu samu ribar duk abin da muka saka a gaba, ba manufarmu meye ake samun kudi ba tare da lissafin yadda lamura za su je su dawo ba.Yanzu kusan duk harkokin da muka kashe su da hannunmu mun koma dillalan wasu akansu.Watakila ma wasu da ba ‘yan Najeriya ba, da mune ke noma kayan gwari da wake da nama da madarar shanu da sauransu mukai Kudancin kasar nan mu sayar, yanzu har ta kai matsayin tun kafin mutum ya yi noma Inyamuri ya zo ya saye gonar tumatur ko albasa ko wake, kaga mutum da gonarsa ya zama wasu yake yiwa bauta, yanzu dabbobi da yawa da mutanan Arewa ke kaiwa Kudu su sayar su samu riba, yanzu Bayerbe ko Inyamuri zai zo Arewa da jakar kudinsa ya sayi saniya ko dan taure ya tafi da abinsa, ka ga duk wata riba an kureta. Kuma babu shigar da zamani a mafiya yawan harkoki irin wadannan.
A ganina irin wannan tunani ya sanya har a harkar Siyasa kowa na son ‘yan Arewa su daskare a waje daya, dukkanmu mu hadu mu zama ‘yan Adawa/Hamayya ga gwamnatin da ba dan Arewa ne ke jagorantar ta ba. Ba laifi bane ace ‘yan Arewa muna tafe tare muna Magana da murya daya akan abin da ya shafi Arewa, amma yanayi na siyasar Najeriya daukar layi daya a Siyasance shi ne babban abin da zai janyo mana koma baya ta fuskar cin ribar Dimokaradiyya matukar ba mune keda gwamnati a hannu ba. Idan dukkan manyan ‘yan siyasa daga Arewa suka kasance ‘yan Adawa ya zama ba muda manufa, kuma ba muda tsari, ai ya zama dole mu shiga a dama gwamnati da mu ana so ko baa so, tunda babu wanda ya isa yace mu ba ‘yan Najeriya bane kuma mu ne muke da yawan jama’a.A tunanina ko da cutar da mu zaa yi saboda muna Hamayya, idan har akwai wasu namu a tare da gwamnati to cutarwa zata zama ana yin hannu yasan na gida, sabanin ace dukkanmu ke adawa da wadanda zasu iya cutar da mu.
A baya lokacin da mutane irinsu Malam Nasiru Elerufai yana minista a gwamnatin Obasanjo, ai dan Arewa ne, kuma ko babu komai ya taimaka wajen daidaita sahun birnin tarayya, direbobin motar haya masu rainawa Hausawa hankali sun shiga taitayinsu, kuma yana daya daga cikin utanen da ake ganin sunyi kokari a gwamnatin Obasanjo.To yanzu da Elrufai ya zama dan Adawa me adawarsa ta haifar? Ai idan har shigarmu gwamnati bata janyo mana cigaba da karuwar arziki ba da cin moriyar ribar Dimokaradiyya ba, to babu shakka janyewarmu daga gwamnati babu abin da zata janyo mana sai bakin ciki da bacin rai kullum, mu yi ta magana akan abubuwan da ba za mu iya sauya tafiyarsu ba, bakinciki da damuwa su lullube tunaninmu.
A ra’ayi na, babban kuskure ne gaba dayan manyan ‘yan siyasa a Arewa su zama suna Adawa da Gwamnatin daba ta dan Arewa ba.Dan shi ba Musulmi ba ne dan Arewa. Ba aibu bane wasu su zama masu hamayya a gwamnatin Demokaradiyya dan a kawo gyara mai ma’ana a harkar tafiyar da gwamnati, haka kuma ba aibu bane wasu su kasance suna cikin gwamnati ana yi da su ko ana so ka baa so.
Babu laifi a samu wasu zakakurai a cikinmu su zama ‘yan Hamayya, su caccaki gwamnatin tarayya ta dinga yin daidai tana so ko bata so, haka kuma ba aibu bane dan wasu muhimman mutane daga cikinmu sun shiga cikin gwamnati dan samar mana da ayyukan cigaba da more rayuwa.Kamar yadda masu magana ke cewa ana yi da kai ya fi ba a yi da kai.Soja ya koma yalofifa. Amma na san wannan batu ne da yake bukatar zurfin tunani da fahimtar ma’anar siyasar Najeriya da kuma zamantakewar da ta hadamu da mutanen kudancin kasarnan.
Wannan kuma tilas a yi hamayya ko da kuwa namu ne dan Arewa yake Gwamnati. Kuskure ne babba wasu ke yi, wai dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari namu ne dan Arewa a ce ba za ayi Hamayya da Gwamnatinsa ba, sun manta Hamayya ce ta kai shi, kuma itace gishirin Gwamnatin Demokaradiyya.
Ya zama dole, kuma ya zama tilas, mu bude zukatanmu da kwakwalenmu, wajen fahimtar Gwamnati da kuma tsari na hamayya. Kar mu zama sakarkaru, ace idan namu ne ke kai, sai muyi kunnen uwar shegu, muna ganin ana yin ba daidai ba, mu kasa yin magana dan gudun kar a zage mu, ko kuma kar a ce mun taba wanda al’umma ke so. Hamayya kusan wajibi ce a tsarin Gwamnatin Siyasa.