Idris Aliyu Daudawa" />

Kutse: Mark Zukerberg Ya Nemi Afuwar Jama’a

Shugaba kuma babban jami’i na Facebook ya nemi gafarar akan wani abu wanda ya faru, akan wani bayanai da ka bayyana ta kafar sadarwa ta zamani, a shafin karshe na wata Jarida, a Ripon Ingila ranar 25 ga watan Marsi 2018.

Shugaban kamfani Facebook Mark Zuckerberg ya dauki sikakken shafi,  a Jaridu tara wadanda ka fi sani a Birtaniya da kuma jaridar Amurka t aranar lahadi, saboda ya bada hakuri akan abin da ya faru na fitar da bayanai na wani laifin da ya faru amma kuma ya shafi wani.

“Muna da aiki na kare duk wasu bayanan ku, idan ba zamu iya ba ke nan bamu kama ci mu yi haka ba’’

Ita dai tallar ta fto a jaridu shida na kasar Birtaniya, har ma da wadda ta fi kasuwa wato Mail tya ranar lahadi, da kuma Sunday Times, da kuma The Obserber, wadanda suka bada labaran da dumi duminsu, har ma da jaridar Newyork Times, Washington Post da kuma mujallar Wall Street Journal.

Zuckerberg ya bayyana cewar akwai shirinas kwakwalwa wanda wani mai bincike jami’a ya yi, abin ya fita ta kafar sadarwata Facebook wadda kuma milyoyin mutane suke amfani da ita, a shekarar 2014’’.

‘’Wannanya taka ka’idar aiki ni kuma ban ji dadin haka ba, shi yasa  nake bada hakuri, saboda muna daukar matakai domin ganin cewar irin hakan bai sake faruwa ba nan gaba’’.

Wannan talla ta nuna bayanan da shi Zuckerberg yayi makon da ya gabata, bayan da al’amarin da ya faru ya sa, sai an yi bincike, a kasashen yammacin Turai da kuma Amurka, daga baya  kuma sai aka aiko ma Facebook akan yadda za a kai ga sasanta maganar, wadda ta shafi hannun jari da kuma yadda farashin ya fadi. Ya kara maimaita cewar shugabar kafofin sadarwa na zamani ta canza dokoki akan abubuwan da ake yin amfani dasu wajen amfani da wani sashe ko bangare, na kafar sadarwa ta zamani, wato applications , don haka ba za a sake  amafani da damar ta samun shiga don amfani da wani sashe ko bangare na kafar sadarwa ta zamani, ta mafani da datar wani ko wasu, wannan abin ba zai sake faruwa ba ko kadan ma.

‘’Muna kuma duba ko wane irin application wanda yake da hanyar samun damar amfani wato (data ) da yawa, kafin mu sa abin. Don haka muna sa ran da akwai wasu.

‘’Idan kuma muka same su, zamu hana su amfani da amfani da Facebook, za kuma mu fadawa duk wanda abin ya shafa’’.

Ba a dai mabaci wani kamfanin Birtaniya ba dangane da amfani da data, Cambridge Analytica wanda ya yi aiki lokaci yakin neman zaben Donald Trump a shekarar 2016. Nan ma an ga laifin  wani mai bincike na jami’ar Cambridge Aledander Kogan, akan duk wani laifin da ya shafi amfani da data, ba akan ka’ida ba. Kogan ya kaddamar da shafin samfurin rayuwa a Facebook, wanda na mutane  270,000  ne, amma sai ya samar da dama ta mutane milyoyi.

Facebook ya bayyana cewar ya sanar da Cambridge Analytica ba tare da sanin shi ba, amma shi Kogan cewa ya yi ana nema ne, a mayar da shi kamar bai san abin da yake ba.

Exit mobile version