Kutungwilar Kifar Da Gwamnatin Buhari Muguwar Aniya Ce – Adesina

Daga Mahdi M. Muhammad,

Fadar Shugaban kasa da ke Abuja ta yi zargin cewa akwai wasu mutane da ke kitsa kutungwilar kifar da zababbiyar gwamnatin farar hula da ke kan karagar mulki a Nijeriya saboda cimma muradunsu na son zuciya.

Fadar ta bayyana haka ne ta bakin mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina, inda ta kara da zargin cewa wasu fusatattun shugabannin addinai da na siyasa da suka hada har da mazan jiya suna ci gaba da yunkuri na tilasta yin canji da karfi da yaji ba ta hanyar da tsarin mulkin dimokuradiyya ya shirya ba wanda kuma hakan ba mai sabuwa ba ce.

A wata sanarwa da ya fitar, Adesina ya bayyana cewa, a yanzu haka masu kulla makirci da kutungwila iri-iri suna daukar shugabannin wasu kabilu da ‘yan siyasa, da nufin kiran wani irin taro, inda za a kada kuri’ar nuna rashin amincewa ga Shugaba Muhammadu Buhari, wanda hakan na iya haifar da rikici a kasar.

Adesina, wanda ya bayyana irin wannan yunkuri a matsayin haramtaccen abu, da kuma cin amana, ya ce, gwamnatin Buhari za ta ci gaba da kasancewa a karagar shugabancin Nijeriya a iya wa’adinta.

Ya ci gaba da cewa, masu tsokanar fada suna fatan cimma muguwar aniyarsu ta hanyar da ba ta dace ba, abin da suka kasa yi ta akwatin zabe a zaben 2019, yana mai gargadin cewa, irin wannan shirin zai iya jawo tashin hankalin a kasar nan.

Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ‘Yan Sandan Sirri (DSS), a ranar Lahadin da ta gabata ta yi magana game da mummunan yunkurin da wasu bata gari ke yi na yin barna ga gwamnati, ikon mallaka da kasancewar kamfanonin kasar. Wanda wasu shugabannin addini da na siyasa da suka gabata suke yi, aniyar ita ce a karshe su jefa kasar cikin wani mawuyacin hali, wanda zai tilasta yin canjin shugabanci mai karfi da rashin bin tsarin dimukuradiyya.”

Ya ci gaba da cwwa, “`Yan Nijeriya sun zabi mulkin dimokiradiyya, kuma hanya daya tilo da za a iya amfani da ita don sauya gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimukuradiyya ita ce ta hanyar zabuka, wanda ake gudanarwa a lokutan da aka tsara a kasar. Duk wata hanyar kuma haramtacciya ce, har ma da cin amana. Tabbas, irin wannan zai iya jawo sakamakon mara kyau.”

“Wadannan mutane da kungiyoyin da aka bata suna nan suna yin hadin gwiwa tare da karfin waje don haifar da mummunar rikici a kasarsu. Amma Fadar Shugaban kasa, wacce tuni ‘Yan Nijeriya suka ba ta iko da izini har zuwa 2023, ta yi alkawarin rike kasar…,” in ji shi a cikin sanarwar.

Exit mobile version