Connect with us

LABARAI

Kwalara Ta Kashe Mutum 61 Yayin Da 50 Ke Asibiti A Yobe

Published

on

Gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar da mutuwar mutum 61 sakamakon barkewar cutar kwalara a cikin jihar. Kwamishin lafiya  Mista Muhammad Bello Kawuwa shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake hira da manema labarai a Damaturu  jiya Juma’a. Ya kara da cewa lalle kwalara ta samu barke wane sakamakon rashin dakin gwajin zawo wanda cutar kwalaran ta haddasa. Ya ci gaba da cewa mutane 906 ne suka barke da zawo tun daga ranar 17 ga watan Satumba ta shekara 2018 a cikin kananan hukumomi guda 5, wanda suka hada da Gujba, Gulani, Damaturu, Fune, Potiskum da kuma Nangere.

“A halin yanzu, akwa sama da mutane 795 wanda suke samu sauki, yayin da guda 50 ke amsar magani a asibiti daban-daban dake fadin jihar. Abun takaici kuma, mun rasa majinyata guda 61 sakamakon rashin zuwa asibiti da wuri don amsar magani.

“Ya yi mana ciwo matuka, ganin yadda jiharmu ta rasa ‘ya’yanta. Muna tabbatar wa mutane cewa za mu yi bakin kokarin mu don ganin mun kiyaye rayukan al’umma,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa hukumar lafiya tare da goyan bayan hukumar lafiya ta duniya WHO da dakin kwaji na asibitin kuyarwa na jami’ar Maiduguri dama hukumar dake kula da cututtuka na Nijeriya dake garin Abuja,  za su yi aiki kafada da kafada wajen yin kwajin cutar zawo.

“Bisa damuwar da muke yi dangane da kula da lafiyar al’ummarmu, shi ya sa muka samu goyan bayan hukomomin kasashan waje. Saboda haka gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar da barkewar kwalara a cikin jihar”, inji shi.

Kawuwa ya danganta barkewar cutar a wasu yankunan da cewa sakamakon shan ruwa sama ne wanda ya sauka a cikin jihar makwannin da suka gabata.

Kwamishinan ya ce, kasancewa an bayyana bullar cutar a jihar Yobe, hukumarsa za ta hada hannu da shuwagabannin addinai da shuwagabannin al’umma da kuma mutanan jihar wajen ganin an magance cutar cikin karamin lokaci. Ya kuma bukaci hukumomin cikin gida dama na waje da kuma gamayyan kananan hukumomin jihar da su kawo kwararru cikin jihar domin kauda wannan cuta ta kwalara.

“Ina rokon kafafan yada lamarai da su yi amfani da wannan dama wajen sanar wa mutane illar kwalara da kuma yadda za a kauce mata ”, in ji shi.

Idan ba a manta ba dai,  a cikin watan Yuli ne gwamnatin jihar Yobe ta bayyana barkewar cutar na kwalara inda aka rasa mutane 13, guda 163 kuma suna asibiti suna shan magani tsakanin watan Maris da kuma watan Yuli ta shekarar 2018.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: