Khalid Idris Doya" />

Kwalejin ATAP Ta Baiwa Nakasassu Guraben Karatu Kyauta

Yanzu haka dai nakasassu a Jihar Bauci sun samu amincewar tallafin yin karatu kyauta a fannon-in ilimin kimiyya da fasaha domin bunkasa ilimi a tsakanin jama’a da kuma shigar da su cikin sha’anin rayuwa don kauce wa nu na su a matsayin nakasassu.
Shugaban kwalejin kimiyya da fasaha, mallakin gwamnatin Jihar ta Bauci, Dakta Sulaiman Mu-hammad Lame, shi ne ya bayyana aniyarsa na ganin an baiwa nakasassun zarafin yin karatu kyau-ta a wannan kwalejin ta ATAP, hade da wasu bukatu da kungiyar nakasassun suka bukata daga gare ta. Kamar samar da dakunan zagayawa wadanda suka dace da guragu da sauran masu buka-ta ta musamman, sai kuma neman a ba su dama a gidan rediyon kwalejin domin su rika yada manufofinsu don gwamnati da sauran jama’a su rika sanin halin da nakasassu ke ciki.
Wakilinmu ya bayyana mana cewar, nakasassun sun samu wannan damar ne a lokacin da suka kai ziyara wa shugaban kwalejin a makon nan, inda suka bukaci tallafinsa da agajinsa. da yake ma-gana kan ziyarar ta su, Hamza Waziri, wadda shi ne shugaban kungiyar kare kima da ‘yanci hade da martabar nakasassu, ya bayyana cewar shigar da bukatar ya zama tilas la’akari da dimbin matsaloli da kuma saniyar ware da aka mai she da nakasassun, yana mai bayanin cewar suna da baiwa da fasahar da Allah ya yi masu, don haka ne ya shaida cewar da zarar suka samu dama za su kyautata rayuwarsu da na jama’an da suke rayuwa a ciki.
Hamza, ya kara shaida wa shugaban makarantar cewar yanzu lokaci ya wuce da za su zo suna neman a tallafa wa nakasassu da tallafi na sadaka ko samar masu da yanayi na bara, ya ce, lokaci ya yi da za su tashi tsaye domin neman hanyoyin inganta rayuwarsu daidai da na kowa.
Daganan kuma, sai ya shigar da bukatu guda uku a gaban shugaban kwalejin ATAP, bukata ta farko ita ce, tallafi kan neman ilimi, sai kuma neman a samar masu da dakunan bahaya daidai da yanayin su, sai bukata ta uku, wacce ita ce, a ba su dama da zarafi wajen shelanta ta su hajar a cikin gidan rediyon da kwalejin ke kokarin kafawa.
Da yake jawabin sa, Shugaban na ATAP, Dakta Sulaiman Muhammad Lame, ya amince da duk-kanin bukatun da kungiyar nakasassun suka bijiro masa da su, inda ya tabbatar musu da cewar, an baiwa dukkanin wani nakasasshe damar zuwa domin yin karatu a wannan kwalejin kyauta, haka kuma ya bayyana cewar, zai dauki nauyin gina bayan-gida guda 20 wadanda zallar su na amfanin masu bukata ta musamman ne, sai kuma ya bayyana cewar bukatar fili a gidan rediyo domin su rika bayyana ababen da suka shafe su wannan ma an ba su damar sa.
Shugaban kwalejin ya bayyana wasu kwasa-kwasai uku da za a fi baiwa nakasassun dama a cikin su a cewar sa, hakan zai bayar da dama a samu hanyar kyankyashe dalibai masu ilimin zamani, fannonin su ne, Chemistry, Mass, da kuma Physics, sai kuma fannonin kimiyya da na fasaha.
Lame, ya kuma shaida cewar, baya ga daukan nauyin karatun, za kuma su samar wa nakasassun dakin kwana ga dukkanin wanda ya samu gurbin karatu a kwalejin, haka kuma ya amince wa kungiyar da su ma su gina karin makewayin, idan suna da bukatar kari a kan guda 20 da shi zai samar.
Lame, ya bayyana cewar, ya bayar da wannan damar ne domin inganta ilimin kimiyya da fasaha a shiyyar Arewa Maso gabas, ya bayyana cewar an yi fintinkau wa yankin a bangaren ilimi domin haka, za su yi duk mai yiwuwa domin dawo da martabar ilimi a yankin.
Don haka ne, ya bayyana masu cewar dukkanin wani nakasasshen da ke son yin karatu ya zo za a ba shi gurbi hade da matarsa hannu bibiyu, domin shi ma ya samu ilimi daidai da dan kowa.
Da yake bayanin wa, LEADERSHIP A YAU JUMA’A, kan yadda suka amshi wannan tallafin hannu bibiyu, hade da nu na godiyarsu ga Shugaban ATAP, Hamza Waziri, Shugaban nakasas-sun, ya bayyana cewar, “Wallahi yau ina cike da murna, kai ba ma ni kadai ba, dukkanin wani mai bukata ta musamman a fadin Jihar nan, murna yake yi, ko da bai da ra’ayin karatu, to na tab-batar maka yana cike da murna, kai bari ka ji, wannan gagarumar nasara ce a garemu, ba mu kadai ba, dukkanin wani nakasasshe a ko’ina yake a fadin Nijeriya, abin ya yi murna ya kuma yi tsalle ne, domin burinmu ya dauko hanyar cika,” a cewarsa.
Ya kara da cewa, “Abu daya da za mu iya cewa ga Dakta Lame, Allah ya saka masa da alheri, Allah ya biya masa bukatocinsa, Ya kuma kare shi da dukkanin karewarsa.”
“Yau kamar Sallah take a wajenmu, kuma a yau mun kafa tarihi a cikin Jihar Bauci, buga-buganmu ya yi nasara, mun dauko hanyar cin nasara don haka muna godiya sosai,” in ji Waziri.
Hamza Waziri, wanda har-ila-yau, dan yi wa kasa hidima ne a wannan kwalejin ta ATAP, ya bayyana cewar yanzu haka sun fara ganin hasken hanyoyin da rayuwarsu za ta inganta, hade ku-ma da yin kira ga sauran bangarorin jama’a da su tabbatar da yin koyi da wannan Shugaban domin tallafa wa mabukata.
Sai ya jawo hankalin dukkanin wadanda za su samu gurbin karatun, da su yi abin da ya kai su makarantar ba tare da aikata ayyukan da ba su kamata ba.

 

Exit mobile version