Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Dake Bauchi Ta Kori Malamai Biyu Kan Aikata Fyade

Daga Khalid Idris Doya,

Kwalejin kimiyya, fasaha da kere-kere mallakin gwamnatin tarayya (FedPoly) da ke Bauchi, ta kori malamai biyu masu suna Adebaye Michael Sunday da kuma Abubakar Musa Baba bisa samunsu da aikata babban laifi na yi wa daliban kwalejin fyade.

Shugaban kwalejin, Arc. Sanusi Waziri Gumai shi ne ya shaida hakan wa ‘yan jarida jimkadan bayan kammala zaman majalisar koli na kwalejin karo na 98 da suka gudanar a karshen mako.

Ya yi bayanin cewa, kesa-kesan din fyaden sun shigo hannun kwalejin ne a ranar 4 ga watan Agustan wannan shekarar inda suka amshi korafe-korafe da daman gaske wanda hakan ya sanya kwalejin kafa kwamiti na musamman domin zurfafa bincike kan lamarin.

Ya ce, bayan kammala aikin kwamitin sun yanke hukuncin korar daliban bayan samun kwararan hujjoji kan zarge-zarge.

Har-ila-yau, majalisar kolin kwalejin ta kuma sallami dalibai 16 da suka gabatar da kwafin bogi na diploma domin samun gurbin karatu a kwalejin, wakazalika, Rector din ya sanar da cewa sun kuma kori wasu karin dalibai 14 bisa kama su da laifin magudi ko satar jarabawa.

Arc. Sanusi Gumau ya nuna damusarsa bisa yadda wasu ‘yan jarida suka yi ta ririta kes din Abubakar Musa Baba na tsangayar koyar da ilimin komai da ruwanka, suka kyale na Adeboye Michael Sunday na tsangayar nazarin ilimin abinci mai gina jiki, alhali dukkanin kesa-kesan iri daya ne ya fyade.

Shugaban ya bayyana cewar dukkanin mata dalibai biyu da aka yi wa fyaden suna da alaka na kusa-kusa da sojoji domin dayan mahaifinta soja ne, a yayin da dayan kuma ‘yar uwanta ta kasance soja ce.

Ya ce, bayan da lamuran suka faru, matan sun gabatar da korafi a rubuce inda kwalejin ta aike da takardar tuhuma ga wadanda lamarin ya shafa domin su mata bayanin ababen da ake zarginsu, ya bayyana cewar bayan amsar da malaman suka baiwa kwalejin wanda bai gamsar da hukumar gudanarwa na kwalejin ba, hakan ya sanya kafa kwamiti domin bin ka’idojin aiki daga bisani majalisar koli ta yanke hukuncin sallamar su.

A cewarsa, sun kafa kwamitin bisa bin dokokin kwalejin tare da daukan matakan da suka dace bisa doron dokan da makarantar ke tafiya a kai.

Ya sanar da cewa a kowani lokaci suna maida hankali wajen ganin dalibai da malamai sun bi dokoki da ka’idojin makarantar, ya kuma yi gargadin cewa ko da wasa ba za su lamunci keta haddin dalibai ko wuce iyakan mamalai a kansu ba.

Exit mobile version