Connect with us

LABARAI

Kwalejin Ilimi A Kwara Ta Bankado Masu Satifiket Din Karya 2,000

Published

on

Hukumomin Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara da ke Ilorin, babban birnin jihar, sun ce sun bankado wasu da suke amfani da satifiket din karya da sunan Kwalejin har guda 2000.

Da yawa daga cikin satifiket din bogin tuni an sami ayyuka da su a wasu hukumomin gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaban Kwalejin, Farfesa Yusuf AbdulRaheem, ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Ilorin a karshen makon nan, ya kuma yi zargin cewa akwai hannun wasu daga cikin ma’aikatan Kwalejin a wajen bayar da satifiket din bogin.

Yusuf AbdulRaheem, ya bayyana cewa jami’ai daga hukumar tsaro ta DSS ne suka bi sawun wani da ake zaton yana daya daga cikin ma’aikatan Kwalejin da a ka kora daga aiki.

Ya bayyana cewa Kwalejin ta nemi ma’aikatar Ilimi ta Jihar, Hukumar bayar da Ilimin baidaya, da kuma hukumar malamai masu koyarwa ta Jihar da su tantance takardun shaidar satifiket na dukkanin ma’aikatansu domin rabewa a tsakanin aya da tsakuwa.

Shugaban Kwalejin ya yi nuni da cewa a bisa hakan ne Kwalejin ta iya tsamo takardun satifiket masu yawa da aka bayar da sunan Kwalejin wadanda kuma duk na bogi ne.

“Sama da takardun satifiket 2000 ne muka gano wadanda aka bai wa wasu daga wannan Kwalejin ta bayan gida. Mun je hukumar SUBEB, Hukumar daukan malaman makaranta da Ma’aikatar Ilimi ta Jihar nan, inda duk muka nemi da su tantance takardun ma’aikatansu. A karshe mun sami da yawansu duk na karya ne. kuma wasu daga cikin jami’an Kwalejin namu ne suke aikata wannan mummunan aikin ta bayan gida.

“Mun maka ma’aikatan namu masu yawa a gaban hukumar tsaro ta DSS saboda sam ba mu da wata matsala da malamai masu koyarwa a Kwalejin namu. A yanzun ya rage ga masu rike da irin wannan satifiket din na karya da su je su wanke kansu a gaban hukumar.

“Amma muna yi wa Allah godiya. A yanzun kowa ya shiga taitayinsa, yanzun da zaran ka je wajen wani ma’aikacinmu da sunan kana neman wani taimako, a take zai gaya maka cewan shi ba shi da ikon yi maka wani abu. A yanzun malamanmu suna shiga cikin azuzuwa tare da dalibansu a cikin farin ciki,” in ji shugaban makarantar.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: