Connect with us

LABARAI

Kwalejin Kimiyya da Fasaha Ta Hussain Adamu Ta Samu Tallafin Gwamnatin Tarayya

Published

on

Kamar yadda manya da kananan makarantun gwamnatin tarayya ke samun kulawar da ta kamata musamman wajen gudanar da aikace aikace daga gwamnatin tarayya.
A zahiri ana iya cewa ita makarantar kimiyya da fasaha ta Hussain Adamu mallakin gwamnatin tarayya dake garin Kazaure ta amfana da aikace-aikace. Da yake zanatawa da manema labarai kwanakin baya a makarantar, magatakardar makarantar Malam Rabi’u Muhammad Danmalan.
Danmalan ya ce makarantar ta samu aikace aikacen ne a karkashin SDG dake ma’aikatar ayyuka da gidaje na gwamnatin tarayya. Rabi’u Muhammad Dammalan ya ce aikace-aikacen da makarantar ta samu sun hada da samar da hanya mai tsawon kilomita uku da rabi, babu shakka wannan hanya ta taimaka musamman yadda ta ba da damar zagaye makarantar cikin sauki.
Makarantar ta Hussain Adamu tana da ‘Campus’ guda biyu inda ake aiwatar da sabbin gine-gine wanda za a a iya gina dakunan gwaje gwaje irin na kimiyya da fasaha.
Haka kuma gwamnatin tarayya duk dai akarkashin SDG ta samar da rijiyoyin burtsatse guda biyu masu amfani da hasken rana daya a dakunan kwanan dalibai mata yayin da daya aka samar da shi a gidajen ma’aikatan makarantar.
Wannan samar da rijiyoyin ya taimaka sosai wajen kawo karshen ruwa amakarantar, sannan kuma akwai fitullun masu aiki da hasken rana da aka sanya a titunan dake cikin makarantar.
Magatakardar makarantar ta Hussain Adamu ya ce, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanje ne ya mayar da ita mallakin gwamnatin tarayya a 2007 bayan wata ziyara da ya kawo makarantar.
Lokacin da suke karkashin gwamnatin jihar Jigawa, suna da kwasakwasai takwas ne bayan an tabbatar da ingancin su tare da bayar da shaida difiloma a kan su.
Rabi’u Muhammad Danmalan ya ce, zuwa yanzu makarantar tana da kwasakwasai 23 wanda aka tabbatar da sahihancin su abin farin ciki takardun shaidar da ake bayarwa ba su da kokwanto akai, akwai na babbar difloma guda takwas, duk wadanan kwasakwasai da ake yi bagaran kimiyya ne da abin da suka shafi injiniya wadannan sashi sune makarantar tafi karfi akai.
Daya ya juya ga malaman makarantar kuwa ya ce babu shakka akwai malamamai masu hazaka da himma domin yanzu haka akwai masu digiri na biyu dana uku kimanin goma shatakwas, da ya wa daga cikin su sun yi karatu ne a kasashen waje.
Ya yi amfani da wannan dama da gode wa TET-FUND domin a wajen ta ne suke samun kudaden karo karatu saboda haka babu abin da za su ce sai godiya ga Allah. Daga karshe ya nuna damuwarsa game da yadda al’ummomin jihohin Jigawa da Kano, musamman matasa ke baya baya da karatu a makarantar da yawa daliban makarantar daga wasu jihohin suke zuwa domin karatu, saboda haka lokaci ya yi da al’ummomin wadannan jihohi za su farka domin zuwa karatu a makarantar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: