Daga Muhammad Awwal Umar
Dalibai dari da ashirin ne kwalejin kimiyya ta gwamnatin tarayya da ke Bida ta tantance dan fara karatun digiri na hadin guiwa da jami’ar kimiyya da ke Minna.
Wannan wani cigaba ne ga dalibai dari biyar da su ka nuna bukatar fara karatun wanda yanzu haka sun yi rajista tun fara shirin a shekarar da ta gabata.
Shugaban jami’ar da ya samu wakilcin darakta mai kula hadakar kwasakwasai na jami’ar, Farfesa Johnson Olusegun Oyefo, ya bayyana hakan a lokacin bukin tantance daliban a babban dakin karatu na Twin Theatre a kwalejin.
Ya jawo hankalin daliban da kar su jefa kan su a harkokin rashin gaskiya a lokacin jarabawa, da kuma wasu miyagun halaye wanda ya sabawa dokokin makarantar, da su zauna lafiya da kowa a cikin makarantar.
A bayanisa, shugaban Poly Bida, Dakta Abubakar Abdul Dzukogi, wanda mataimakinsa a bangaren gudanarwa ya wakilce shi, Dakta Sani Man-Yahaya, ya baiwa sabbin daliban tabbacin za a samu lokacin koyarwa da ilmantarwa wadatacce.
Ya nemi daliban da su yi anfani da wannan damar na samar da shirin dan su cin ma burinsu na kasancewa masu anfani ga kasa da duniya baki daya.
Darakta mai kula da hadakar kwasakwasai na kwalejin, Dakta Ndako Yahaya, ya yabawa nasarar da aka samu tsakanin kwalejin da jami’ar kimiyyar kan wannan shirin, inda ya bayyana shugaban kwalejin a matsayin mai kwazo da kokarin ganin an samu nasara akan shirin.
Yace duk da matsalolin da kwalejin ke fuskanta, kwalejin na yaye dalibai da dama sabanin wasu makarantu da ke hadin guiwa kan kwasakwasai da jami’ar.
Wasu daliban da muka zanta da su, sun nuna jin dadinsu akan yadda shugabannin kwalejin ke samar da kwasakwasan da kwalejin ba ta da su daga wasu jami’o’i musamman darussan digiri dan anfanar al’umma bisa jagorancin shugaban kwalejin. Inda suka baiwa dalibai yan uwansu shawara su zama masu bin doka da oda da kauracewa duk wani abinda zai janyo tashin hankali a kwalejin, dan ganin sun kammala karatun su akan lokaci da samun sakamako mai kyau.