Kwalejin Legal Ta Misau Na Bukatar Tallafin Hukumar TETFUND –Dr Auwal Amba

A kwanakin baya ne Kwalejin nazarin Shari’a da addinin musulunci da ke Misau wato College for Legal and Islamic Studies ta sami sabbin shugabannin gudanarwa, inda aka nada DR. AUWAL IBRAHIM AMBA na Jami’ar Jihar Bauchi da ke garin Gadau a matsayin sabon shugaba da sauran jagororin da za su shugabanci makarantar na tsawon shekaru hudu. Inda aka nada Malam Garba Musa Gar a matsayin rijistara da Malam Mohammed Dahiru Ibrahim a matsayin Bursar da Malam Lamido Mohammed Abdullahi a matsayin mai lura da dakin karatu. Don haka wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI a Bauchi, MU’AZU HARDAWA, ya tattauna da Dr. Amba a ofishinsa da ke harabar makarantar a garin Misau game da yadda za a ciyar da makarantar gaba musamman ganin ta fara karatun nazarin takardar shaidar Digiri a karkashin jami’ar Bayero da ke Kano, wato BUK. Ga yadda hirarsu ta kasance:

Wane kalubale wannan kwaleji ke fiskanta game da ci gaban karatu bayan kun kama aiki?

Da sunanan Allah mai rahama maijin kay sunana Dokta Auwal Ibrahim Amba ni mutumin misau ne na yi karatu a wannan makaranta mai dimbin tarihi wacce ta jima tana horas da dalibai daga kowane sashe na wannan kasa, ta horas da mutane dabam dabam da suka hada da malaman makaranta da alkalai da lauyoyi da malaman addini da ma’aikatan ofis da sauran su. Kuma na dawo yanzu ina jagorancin makarantar tun watan daya inda na taho daga yadda nake aiki a jami’ar Jihar Bauchi da ke garin Gadau kuma na yi aiki wurare da dama amma yanzu na dawo gida domin bayar da gudummowa ta don ci gaban ilmi a wannan makarantar, saboda ba abin da mu ka sa a gaba sai hidima wa ilmi saboda abin da muka koya kenan tun farko.

Wannana kwalejin nazarin addinin musulunci da shari’a ta Misau makaranta ce mai tarihi wacce ta kusa shekara 40, don haka zuwa na shi ne na nemi bunkasa makarantar ta hanyoyi uku da suka shafi gine gine da wuraren karatu da kayan aiki da inganta ma’aikata don su ji dadin aiki su lura da aikin su zuciya daya da amana. Na uku shine muna kokarin fadada abin da muke karantarwa. Don haka yanzu muka fadada wajen yin digiri a harshen hausa da nazarin addinin musulunci da tallafin jami’ar Bayero da ke Kano wadanda sune ke shirya duk wani karatu na digiri biyu da muka fara a wannan makaranta kuma su ke lura da karatun tare da bayar da takardun shaida na jami’ar Bayero da ke Kano mu aikin mu karantarwa ne kurum da lura da yadda ake gudanar da ayyukan cikin nasara.

Nan ba da jimawa ba kuma idan muka daidaita komai za mu bude karatun digiri a sauran sassa da suka kunshi nazarin harshen turanci da tarbiyya da ilmi da sauran fannoni da muke karatu a kan su saboda haka muna bin gwamnati domin ta bamu dukkan abin da muke bukata saboda wannan gwamnati ta sanya ilmi a gaba kuma tana tallafawa ilmi, don haka muke iya kokarin mu wajen ganin mun bunkasa darussa da fadada ilmi saboda gwamnati ta sa wannan batu a gaba wajen tabbatar da haka muke tabbatar da ma’aikata sun rike aiki da amana da zuciya daya.

 

Yaya ku ke gudanar da karatun digiri musamman ganin yadda jami’o’i ke da karancin guraba?

Abin da mutane ke nuna damuwa shi ne ganin muna karatun Difloma da NCE ne kuma sun ji muna yin digiri, abin da basu gane ba komai a wannan makaranta muna yin sa ne kamar yadda jami’ar Bayero ta tsara na sai an yi JAMB an samu darasin lissafi da turanci da sauran darussan da aka tsara. Wasu na ganin ci baya ne karatun digiri a wannan makaranta, alhali idan mutum ya yi digiri kamar ya yi a jami’ar Bayero ne saboda karatun ba zai banbanta ba kuma ka’idojin wannan makaranta sun fi sauki saboda babu masu nema da yawa a nan karatun yafi sauki saboda karancin dalibai a aji fiye da na jami’a mu karatu ne namu idan mutum ya yi karatun digiri a wannan makaranta daidai yake kamar ya yi a Jami’ar Bayero, kuma an fi samun sauki wajen shiga makarantar a kan jami’a haka takardar shaida iri daya ce da ta jami’ar Bayero.

 

Wace matsala ka ke ganin ta damu makarantar a halin yanzu kuma ka ke son ka magance ta?

Matsalolin da muke fiskanta shi ne yadda wasu malamai ke wasa da aiki lamarin da a halin yanzu mu ke son ganin kowa ya ci gaba da rike aikinsa bil hakki da gaskiya. Kuma muna ci gaba da kokarin ganin mun tanadar da dukkan kayan aiki da nazari da ake bukata don ci gaban karatun kowane sashe na wannan makaranta. Bayan haka kuma muna kokarin ganin ma’aikata kowa ya rike aikin sa da daraja da muhimmanci da amana don wasu suna sakaci da aikin su. Muna son inganta kayan aiki da kuma samar da duk wani kwas da ya kamata ace an shigo da shi an kuma inganta shi. Burinmu shin e kafin mu bar wannan makaranta kowane ma’aikaci ya rike aikin sa da muhimmanci kuma mu tabbatar da kowa na aikinsa yadda ya dace.

 

Yaya batun ingancin kwasa-kwasai da lura da yadda hukuma ke tantance su?

Bama gudanar da karatu sai hukumomi sun tantance kowane kwas, kamar yadda kowa ya sani akwai hukumomi da suke tantance kwasa kwasai kuma bama fara karatu sai mun tabbatar irin wadannan hukumomi sun zo wannan makaranta sun duba kayan aiki da malamai da duk wata ka’ida da aka sa sun tabbatar komai ya inganta sun amince kafin mu ci gaba. Don haka duk wani karatu da muke da shi a wannan makaranta gwamnati ta amince da shi kuma takardun mu suna karbuwa a kowane sashe na duniya a fannin aiki ko a fannin ci gaba da karatu. Wannan makaranta duk inda mutum ya nuna takardar mu ana karbar ta kamar yadda ake amincewa da duk wata takarda da makarantar da aka amince da ita ke bayarwa. Don haka duk wata ka’ida muna cika ta da kuma tabbatar da dalibai da malamai kowa ya bi doka ya yi abin da ya dace don gudanar da karatunsa a wannan makaranta lamarin da ya sa wannan makaranta ke da tarihi mai kyau wajen gudanar da ayyukan ta na yau da kullum kamar yadda kowace makaranta a duniya ke ayyukanta don ciyar da ilmi gaba.

 

Akwai korafi da wasu dalibai ke yi na kara kudin makaranta me za ka ce kan wannan batu?

Ko dalibai ka tambaya za ka samu bayani daga wajen su ana biyan kudin makaranta kamar na Islamiyya ne a wannan makarantar, alhali akwai bukatar kudi don gudanar da wasu ayyuka don ci gaban makarantar. Kowa ya sani a Jihar Bauchi ba makarantar da ake biyan kudi kamar na Legal Misau kuma idan ka yi hira da dalibai za su gaya maka karin kashi goma cikin dari da muka yi ya taimaka wajen inganta karatu a wannan makaranta kuma ba yadda karin da muka yi ya taimaka wajen ciyar da karatun gaba. Bayan haka karin da muka yi har yau duk yawan manyan makarantun da ake da a jiha namu shine kasa saboda kar dalibai su ga an tsawwala, kuma kowa ya sani muna iya kokari wajen ganin kowane dalibi ya samu biyan kudin makaranta ba tare da ya fiskanci matsala ko dakatarwa daga karatu ba.

 

Asusun tallafawa ilmi na kasa wato TETFUND na aiki a manyan makarantu kuna samun tallafin su?

Muna fiskantar matsala saboda wannan makaranta bata amfana da tallafin asusun Tetfund da ke taimakawa makarantun gaba da sakandare don haka muke da karancin tallafin kuma yanzu muke neman ganin an sanya mu cikin wannan shiri. Muna fatar ganin wannan hukuma da ke lura da tallafawa ilmi ta sanya mu cikin wannan shiri ta hanyar lura da yadda mu ke gudanar da ayyukan mu. Don haka ba wani aiki da wata makaranta ke yi wanda ba ma yi a wannan makaranta wajen bunkasa ilmi, amma mu wannan makaranta bama samun tallafin wannan hukuma ta asusun bunkasa ilmi na TETFUND don haka muke rokon wannan hukuma ta lura da gudummowar da muke bayarwa wajen inganta ilmi. Don haka muke son a sanya mu cikin makarantun da suke cin moriyar ayyukan wannan hukuma kamar yadda ake yi a wasu makarantu ko jami’o’j da ke kasar na. A yanzu kokarin mu shi ne na ganin wannan hukuma ta taimaka ta shigar da mu cikin tsarin ta na tallafawa manyan makarantu don mu samu damar bunkasa karantun da muke yi fiye da yadda muke yi a halin yanzu. Wannana gwamnati ta damu da ilmi don haka ya kamata a ce wannan gwamnati ta sa kowace makaranta a karkashin wannan tallafi don mu ci gaba sosai kamar yadda saura suka ci gaba.

Musamman a fannin tura malamai makaranta a cikin kasa da wajen ta da kuma gina wuraren da ake bukata da samar da kayan aiki irin na zamani da sauran gudummowa da TETFUND ke bayarwa muna kira da babbar murya ga shugabannin wannan hukuma su taimaka mana da fata Allah ya mana jagora yasa mu dace su ji wannan kira su amsa mana su shigar da mu cikin ayyukan da suke yi.

Exit mobile version