Kwalejin Tarayya Ta Ƙaryata Batun Janye Yajin Aiki

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Hukumar gudanarwa na Kwalejin gwamnatin tarayya da ke Bauchi ta nisanta kanta da wani sanarwa da ake ta yayaɗawa kan batun cewar hukumar makarantar ta fitar da sanarwar dawowa bakin aiki, tun bayan da ƙungiyar malamai wato ASUP da wasu sashi na ma’aikatan kwalejin suka faɗa yajin aiki yau sama da wata uku kenan.

A wani sanarwa da hukumar makarantar ta fitar wacce ta watsa duniya ta bayyana cewar “hankulanmu sun karkata kan wani sanarwar da aka ce wai hukumar gudanarwa na kwalejin tarayya da ke Bauchi ta fitar na batun dawowa daga yajin aiki. Sanarwar wacce kuma aka danganta ta da rijistan wannan kwalejin Hajiya Rakiya Usman Maleka wannan sanarwar da ya yi ta yawo a kafafen sadarwa karya ne kawai” a cewar hukumar makarantar.

Sanarwar wacce ta fito daga kwalejin  ɗauke da sanya hanun kakakin kwalejin Muhammad Rabi’u Wada ya ci gaba da cewa “a sanarwar an ce wai makarantar za ta dawo aiki a ranar jiya. Ana kiran ɗalibai da su gaggauta dawowa makatanra domin ci gaba da ɗaukan darasi”. In ji Rabiu

Sai ya yi amfani da damar ya shalanta wa duniya cewar har zuwa yanzu dai makarantar bata dawo daga yajin aikin da ake ci gaba da yi ba, yana mai kira ga iyaye, ‘yan uwa da sauransu da su sanar da ‘ya’yansu domin kauce wa tasowa daga gidajensu don dawowa alhalin makaranta bata dawo ba, “wasu suna nisan duniya ko wasu garuruwa idan suka dawo alhali ba a dawo yajin aiki ba, abun bai yi kyau ba”. A bisa haka ne aka shalanta cewar yajin aiki dai ana ci gaba da ƙoƙarin shawo kansu.

Inda sanarwar ta bayyana cewar da zarar makarantar ta dawo za su sanar ta hanyoyin da suka saba sanarwa, amma jama’a su kauce wa jin maganganu daga kafefen sadarwar zamani domin kauce wa ruɗu.

Kwalejin dai ta nisanta kanta gami da barranta da wannan sanarwar da aka ce ta fitar na dawowa bakin aiki tana mai bayyana cewar hanyoyin sanarwarta suna buɗe da zarar aka shawo kan matsalar za su sanar.

 

Exit mobile version