Daga Aliyu M. Kurfi (PhD),
Tushen Kasidar
Tun kafin masu karatu su yi nisa za mu so su fahimci musabbabin samar da wadannan shawarwarin da kuma dalilan samar da ita kanta wannan kasida tamu, wadda ke kunshe da su shawarwarin namu. Dalilan Samar da Tsarin ‘Kwali Jari’ ‘Yan’uwa masu karatu, samar da shawarwarin dake a cikin wannan kasida ya biyo bayan wata ziyara ce da wani tsohon dalibina ya kawo mani tun a ‘yan shekarun baya. Dalilinmu na wallafa kasidar kuwa yana da nasaba da ziyarar da wasu matasa daga karamar hukumarmu suka kawo mani, ba da dadewa ba.
A lokacin ziyarar tasa ya sanar da ni cewa ya zo ne domin in taimaka masa ya samu mafita daga matsalar da yake fama da ita ta rashin aikin yi tun bayan da ya kammala karatunsa na jami’a. Ya sanar da ni cewa, yana cike da nadama dangane da karatun jami’a da ya yi, saboda kuwa a sanadiyyar karatun nasa ne sana’arsa ta kafinta ta shiririce, a inda har ta kai ga ya sayar da kayan aikinsa ya kuma saki shagon sana’arsa; watau dai a iya cewa ya yi Kamun gafiyar Baidu. Bayan ya gama yi mani bayaninsa, na fahimci dai manufar wannan ziyara tasa ita ce bukatar taimakona domin samar masa aikin yi. Bisa ga wannan fahimta tawa, sai nan take dabara ta fado mani, domin haka sai cikin lalama na tambaye shi ko yana da banki wanda ya ke hulda da shi. Shi kuwa ya amsa mani cewa yana da shi. Saboda haka ne, ba tare da bata lokaci ba, na shawarce shi da ya je ya samu Manajan bankin nasa, ya bukaci taimakonsa na samun rancen kudi, domin yin sana’a. Na nemi shi tsohon dalibin da ya sanar da Manajan cewa, a shirye yake ya bayar da takardunsa na digiri da na shaidar yin hidimar kasa, a matsayin jingina.
Mun sani dai, a ka’idar banki, jinginar da takardun shaidar kammala makaranta zai iya kasancewa wani abu sabo, wanda mai yiwuwa su kansu ma’aikatan bankin ba su taba jinsa ba. Domin kuwa sanin kowa ne, bankunamu sun fi amincewa da takardun shaidar mallakar fili ko gida, a matsayin jingina, domin bayar da rance; wadanda kuwa shi tsohon dalibin, a iya sani na, a lokacin ba ya da su. Maikaratu, saboda aiki da umurnina, nan take wannan matashi, bawan Allah, ya bazama zuwa banki, ya kuwa yi sa’ar ganin Manajan ya kuma yi masa bayani, kamar yadda na umurce shi. Sai dai watakila kamar yadda mai karatu zai zata ita wannan bukata ta tsohon dalibin zai yi wuya ta samu karbuwa ga kowane banki. Haka kuwa abin ya kasance domin kuwa bayan dawowar matashin daga banki ya shaida mani cewa babu wata amsa mai gamsarwa da ma’aikatan bankin suka ba shi, illa dariya da suka yi ta yi masa, domin kuwa mai yiwuwa ga zatonsu wannan tsohon dalibi ya zautu, saboda rashin aikin yi.
Ganin haka ne fa nan take a cikin bacin rai na sanar da matashin cewa, da yardar ALLAH za mu yi iya kokarinmu har sai mun ga cewa takardun shaidar kamalla manyan makarantu da ke a hannun matasanmu sun yi daraja da tasiri a wannan kasa. Daga nan na roke shi da ya yi hakuri, ya bani lokaci domin neman mafita, wadda kuwa wannan mafita ita ce ke a gaban masu karatu a halin yanzu. Hakika, a matsayinmu na masu koyarwa a babbar makaranta, ya kamata mu dauki kawunanmu tamkar masu yin sana’a domin kaiwa kasuwa mu sayar. Saboda haka idan har abin da muka sana’anta, watau daliban da muka yaye, suka rasa mai saye ta kai ga har sun yi kwantai an karyar da farashinsu, to mu sani mu malamansu ne a ka wulakanta, amma ba su yayayyun daliban ba.
Saninmu ne cewa, saboda wulakanci, a yau dalibanmu wadanda suka kammala manyan makarantu ta kai ga kome kankantar albashi karba suke yi, ido a rufe. Dalilan Wallafa Kasidar Yanzu kuma sai dalilin samar da kasidar. Samar da ita wannan kasida ya biyo bayan wata ziyara ce da wani gungun matasa, daga karamar hukumarmu ta Mashi, a Jihar Katsina, su ka kawo mi ni kwanan baya. Lokacin wannan ziyara matasan sun zo mani da wata wasika wadda a ciki suka nemi amincewata da in kasance daya daga cikin iyayen kungiyarsu, mai suna ‘Kungiyar Matasa ‘Yan Asalin Karamar Hukumar Mashi da Suka Kammala Manyan Makarantu’. Manufar ziyayarar tasu suma ita ce neman agajinmu dangane da matsalar rashin aikin yi da matasa ke fama da ita. A lokacin da muke tattaunawa da wadannan matasa namu dangane da matsalar da ta kawo su, na yi nasarar jawo hankalinsu domin su fahimci cewa yanzu fa babu wata mafita ga matasanmu illa su samu jari wadatacce, domin fara sana’a, saboda ganin wahalar da samun aikin gwamnati ke yi.
A karshen tattaunawar tamu, matasan dai sun nuna sha’awarsu ta ganin sun tsayu da kafafunsu, a inda har daya daga cikinsu ya bayyana mana cewa shi da zai samu jari, babu sana’ar da zai yi illa ta safarar busasshen nama zuwa Kudancin Nijeriya, saboda kuwa a lokacin da ya ke yin hidimar kasa ya sadu da wani matashi da ya fito daga 10 Kudancin Nijeriya, wanda ya nemi su yi hadin guiwa domin yin fataucin busasshen nama zuwa yankin Kudu, wanda ya ce suna da matukar bukata.
Daga karshe dai na yi wa wadannan matasa alkawarin wallafa dan littafi da zai taimaka wajen magance matsalar tasu. Saboda fatar da muke da ita ta samarwa matasan da suka kammala manyan makarantu mafita ya sa muka dauki lokaci mai tsawo muna nazari dangane da dabarun da za su taimaka wajen ganin cewa takardu, ko mu ce KWALAYE na shaidar samun ilimi daga manyan makarantu sun yi kima da daraja. Cikin taimakon Ubangiji, mun yi nasarar samar da wannan hanyar wadda muke fatar ta kasance mafita mai dorewa ga matasan. Mun sanyawa mafitar suna ‘CERTIFICATE FOR LOAN’, wadda a Hausa muka yi wa lakabi da ‘KWALI JARI’.
Manufar wannan kasida a dunkule dai ita ce, jawo hankalinmu dangane da fa’idojin da ke akwai wajen samarwa matasa wadanda suka kammala manyan makarantu jari, ta hanyar basu rancen kudade, domin samar da kananan masana’antu da suka dace da karkara. Muna so a lura cewa, jihohinmu sun dade suna yin asara mai yawa, saboda rashin ingantattun dabaru na bayar da rance ga mabukata, da kuma gazawarsu na yin kyakkyawan amfani da dubban matasa, masu jini a jika, wadanda suka kammala karatunsu a manyan makarantu.
Har wayau, saboda yawan wadannan matasa, mu sani, ko jarin yin noma aka samar masu yawansu ya isa su ciyar da jihohinmu. Gaskiyar magana dai ita ce, a yau babu wata kasa a wannan duniya tamu da za ta bunkasa idan har ta rasa yin kyakkyawan amfani da matasanta. Shin, ta wace hanya mu ‘yan Arewa za mu fita daga wannan kangin da muke ciki na rayuwa da talauci, bayan kuwa matasanmu ba su da aikin yi, har ma idan suna da shi, aikin nasu ba wanda zai taimaka wajen gina kasa ba ne, sai ma ya kashe kasa? Muna da tabbaci cewa, saboda yawan wadannan matasa, da kuma ilimin da suke da shi, har idan aka samar masu da jari, domin yin sana’a, yankinmu da kasa baki daya za su share hanya ta ci gaba. Fa’idar Tsarinmu Ga Gwamnatin Jiha Fa’idojin da za a samu idan aka yi aiki da shawarwarin namu, ba ga matasan kawai za su tsaya ba, domin kuwa su kansu gwamnatocinmu, da al’ummominmu, akwai fa’idoji masu tarin yawa da za su samu. Ga wasu daga cikin fa’idojin da gwamnatoci za su samu:
- Mu sani yin amfani da shawarwarin namu zai rage nauyin da yake a kan gwamnatocin jihohi, dangane da samar da aikin yi ga matasa da suka kammala manyan makarantu.
- Yin amfani da tsarin zai magance yawaitar daukar matasa ayyukan wucin-gadi, irin su N-Power da casual.
- Haka kuma tsarin zai taimakawa shugabanni, musamman Gwamnoni samun nasara a inda takwarorinsu da suka yi mulkin jihohinmu a baya, suka gaza.
- Tsarin zai bayar da dama ga jam’iyya mai mulki ta cika daya daga cikin alkawuranta, watau na samar da aikin yi ga jama’a.
- Tsarin zai samar da hanya ma fi sauki ga gwanatocin jihohi ta raya karkara da kuma rage kaurar matasa zuwa birane.
- Tsarin zai kuma samar da gudumuwa mai dorewa ta hanyar yin amfani da matasa wajen gina jihohinsu, da ma kasa baki daya.
- Tsarin namu zai fito da wata sabuwar hanya ta samun kudaden shiga ga jihohi musamman daga harajin masana’antu wadanda matasan za su samar.
- Hakan zai taimaka wajen samarwa kananan ma’aikata da leburori ayyukan yi, da habakar kasuwanci a jihohi, saboda yawaitar kananan masana’antu a karkara (cottage industry).
- Aiwatar da tsarin zai taimaka wa gwamnati mai ci wajen samun goyon bayan matasa.
- Tsarin zai magance matsalar rashin biyan alawus ga wadanda gwamnati ta dauka aiki na wucin-gadi a yanzu. · Ta hanyar yin amfani da tsarin namu kudade za su zagaya cikin karkara, su kuma shiga hannun jama’a, saboda samun aikin yi ga jama’a da habakar ciniki a jihohi.
- Tsarin zai magance matsalar daukar aiki wanda zai ba gwamnati damar fuskantar matsalolin gina al’umma.
- Yin amfani da tsarin zai taimaka wajen habakar masana’antu da zuba jari a cikin jiha.
- Tsarin zai cusa kishin kai ga matasa, saboda yanzu za su san zafin nema.
- Haka zai taimakawa gwamnati wajen magance yawan daukar ma’aikata ya kuma rage yawan abin da gwamnatoci ke kashewa na kudaden albashi da sallama. Fatarmu dai ita ce, su kansu matasa da ke yin aikin gwamnati a halin yanzu, su ajiye aikinsu, domin amfana da rancen.
- Hakika duk gwamna mai mulki da ya yi aiki da wadannan shawarwari da muka bayar zai bar tarihi a jiharsa ya kuma samu tagomashi, saboda kuwa mutanensa za su ci gaba da tunawa da shi har abada, dalilin kawar da rashin aikin yi da yakar talauci da ya yi.
- Muna da tabbacin cewa wadannan dabaru ko mafita da muka samar, sun sha bamban da irin hanyoyin samar da rance da gwamnatocinmu ke amfani da su domin kawar da talauci a wannan yanki. Maikaratu akwai sauran fa’idoji da gawamnatoci za su samu da basu misaltuwa, wadanda zai yi wuya mu iya kawo dukkansu a nan.