Kwalliyar Fuska Ta Birgewa

Kwalliyar Fuska

Daga Bilkisu Tijjani Kassim,

Masu karatu sannunmu da sake haduwa a wannan makon. Yau filin naku zai yi duba ne ya ga shin wace irin kwalliya ya kamata uwargida ta yi wa maigida?

Uwargida ya kamata kisan irin kwalliyar da yakamata kiyiwa maigida domin jan hakalin maigida gareki,

Yadda ake kwalliya amma ba wadda za ta yi yawa haba uwargida, yakamata ki yi tanadi.

Hoda, Janbaki, Man baki, da Gazal, su kadai sun ishe ki yadda za ki gyara fuskarki, kwalli. Bayan uawargida kin fito daga wanka kin shafa mai kin sa kayanki kafin ki daura dan kwalinki sai ki dauko Hodarki ki sa soson dake cikin Hodar, sai ki dan gogo Hodar a jikin soson Hodar, daga nan sai ki shafa a gefan kowanne kumatunki, sannan ki kara gogawa ki shafa a goshinki, daga nan sai ki dan fara goga soson a kumatunki daya sai ki goggoge gefen fuskarki, sannan ki koma daya gefan shi ma ki goggoga kamar yadda kika yi daya bangaren.

Daga nan sai ki kuma goshinki shi ma ki goge shi gaba daya, sannan sai kasan bakinki, wato habarki, sai ki dan gogo Hodar ki shafa shi ma ki goge shi gaba daya, daga nan kuma sai ki hade fuskarki gaba daya ki goge ko ina har sai kin ga ta hade gaba daya ta yi kyau ba inda ya yi dabbabre-dabbare, daga nan kin gama da shafa Hoda. Sai kuma  ki dauko janbakin ki dan gyara bakinki kafin ki shafa waton idan bakinki yadan bushe sai ki dan jika shi haka kamar ki sa dan mai kadan ko kuma dan saka harshe a kai ki hada fatar bakin kidan murza sannan ki shafa jan bakin ki shafa shi daidai yadda ba zai hawo sama ba daidai iya cikin lebenki, ki gyara shi yadda zai yi daidai ko ina ba yadda wani zai fi wani ba, sannan ki shafa kwalli a idonki shi ma kidan zizara shi yadda zai yi kyau, ba wai yadda zai sauko kasa ba.

Daga nan sai ki dan samu abin taje gira kidan taje ta kuma ki dan gyara ta yadda za ta yi kayu za ki ga ta zama siririya haka. Shike nan kin gama kwalliyarki sai daurin dan kwalli zuwa sati mai zuwa.

Exit mobile version