Gabanin fara gasar cin kofin kwallon Hockey ta Afrika na shekarar 2025 da aka shirya gudanarwa tsakanin 11 zuwa 18 ga watan Oktoba a kasar Masar, shugaban hukumar kwallon Hockey ta Nijeriya (HFN), Injiniya Simon Nkom, ya bayyana kwarin gwiwar cewa tawagar maza da mata na Nijeriya sun yi shiri sosai don tabbatar da samun nasara a gasar da kuma samar wa kasa abin alfahari.
Da yake jawabi a Abuja bayan wasan sada zumunci da aka yi a filin wasa na Hockey Pitch, Package B, Moshood Abiola National Stadium, Nkom ya bayyana shirin da hukumar ta ke yi shirye-shiryen tunkarar gasar da aka tsara don tabbatar da cewa yan wasa sun cika duk wasu ka’idoji da ake bukata domin gudanar da wannan gasa mai daraja ta Nahiyar.
A harkar wasannin, Hockey, kwallon hannu, ko kwallon kwando, motsa jiki shine mafi mahimmanci, shi ya sa muka fara don karfafa yan wasan don fuskantar kalubalen dake gabanmu inji shi, ya kara da cewa wannan ba wasan cikin gida ba ne, gasar cin kofin Afirka ne, kololuwar gasar kwallon Hockey a nahiyar, mun yi aiki tukuru wajen tabbatar da cewa yan wasan a shirye suke, kuma muna da kwarin gwiwar cimma nasarar kammala gasar,” in ji shi.
Ya kara da cewa yan shekarun da suka gabata, an yi shakku kan dorewar wasan Hockey a Nijeriya, amma yanzu tawagarmu ta mata ita ce ta zo matsayi na 3 a Afirka, yayin da tawagar maza ke matsayi na 4, wadannan nasarorin sun nuna irin yadda muka himmatu wajen ganin mun kara inganta wannan wasa a Nijeriya.