Kwamandan ‘Operation Lafiya Dole’ Ya Yabawa Kungiyoyi Masu Zaman Kansu

A jiya ne aka gabatar da taron hukumomin tsaro na kungiyoyin agaji masu zaman kansu a Hedikwatar ‘Operation Lafiya Dole’ dake garin Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.

Taron wanda Kwamandan ‘Operation Lafiya Dole’ din ya kira, Manjo Janar Rogers Nicholas, ya samu halartar manya da kananan kungiyoyin masu zaman kansu wadanda ke aikin bayar da tallafi ga al’umma a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.

Manjo Janar Nicholas ya yaba da irin rawar da wadannan kungiyoyi suke takawa wurin kai agaji ga al’umma, musamman ma wadanda ke gudun hijira sakamakon wannan rikici na Boko Haram.

Kwamandan ya bukaci kungiyoyin da su rika sa lura a yayin gudanar da ayyukansu, domin an fara samun bata gari, wadanda ke ayyyuka ba bisa tsari ba, kuma ba tare da sun kasance kungiyoyi masu rajista ba.

Ya gargadi irin wadannan kungiyoyi da su yi rajista nan da makonni biyu ko kuma su fuskanci matakin hana musu shiga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira tare da hana su wucewa ta wuraren da sojoji ke gadi.

Kwamandan ya roki dukkan kungiyoyin agaji dake aiki da su tabbatar da cewa su na yin amfani da motoci masu lafiya wajen jigilar kayan agaji domin gujewa yadda motoci ke lalacewa cikin daji har ‘yan Boko Haram su samu sukunin bullowa su sace kayan dake ciki.

Exit mobile version