Daga Rabiu Ali Indabawa
Kwamandan sojojin Sudan ta Kudu da aka kama su da laifin yi wa wasu mata masu aikin agaji fyaɗe ya mutu a gidan waƙafi. An samu gawar Luka Akechak a gidan wakafin da yake tsare.
Kwamandan sojojin Sudan ta Kudu wanda ƙarƙashin kulawarsa ne aka zargi sojoji da laifin kashe wani ɗan jarida, da kuma yiwa a ƙalla mata ma’aikatan agaji huɗu na ƙasa da ƙasa fyade a shekarar da ta gabata.
Da farko dai an samu gawar Lautanal Luka Akechak, mace a inda ake tsare da shi tun sama da mako guda da ya gabata, amma sai ranar Juma’a aka fitar da rahotan mutuwar.
“Luka Akechak dai ya mutu. Kuma mutuwar ajali ce.” A cewar Domic lokacin da yake magana da’yan jaridu.
Shine babban wanda ake zargi a ta’asar da sojojin Sudan ta Kudu suka aikata, wanda hakan yake nuna yadda yake da matukar wahala wajen gabatar da waɗanda ake zargin take haƙƙin bil Adama ga shari’a a ƙasar, wacce ta share shekaru hudu tana fama da tashin hankali.
Ɗaya daga cikin matan da aka yiwa fyaden ta zargi Akechak da umartar sojojin dake karkashinsa su yiwa mata ma’aikatan agajin fyade a otel din Terrain dake Juba cikin watan Yulin shekarar 2016.