Kwamandan ’Yan Sanda Na Shiyya Ta DayaYa Fara Rangadi

Domin tabbatar da tsaro da kuma sauke nauyin da aka dora ma sa, babban kwamandan ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya a jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Ibrahim ya fara za ga gundumomin ‘yan sanda da suke shiyya ta daya mai cibiya a Zariya.

Baya ga jami’an ‘yan sanda da suke karkashinsa, kwamandan kan saurari jawaban shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya da kuma kungiyoyin al’umma da aka kafa su domin ci gaban al’umma da kuma kare mutuncinsu ta ko wane bangare.

A jawabinsa a ofishin ‘yan sanda da ke Dan Magaji, Alhaji Abdullahi Ibrahim ya tunatar da daukacin al’umma da suka tarbe shi a lokacin da ya je wannan ofishi cewar,batun tsaro, batu ne da kowa ke da hannu a

kai, wato kamar yadda ya ce ba a bar matakan tsaro ga jami’an ‘yan sanda kawai ba.

Kamar yadda ya ce, in har ana son a sami ingantaccen zaman lafiya da kuma tabbatar tsaron lafiya da kuma dukiyoyin al’umma, wajibi ne, inji shi, a hada hannu da ‘yan sanda, ta bayyana ma su maboyar bata-gari

da kuma ba su duk shawarwarin da za su tallafa ma su, su sami damar sauke nauyin da aka dora ma su a cikin sauki da kuma Alhaji Abdullahi Ibrahim ya juya ga iyayen yara da suke shiyya ta daya da kuma jihar Kaduna baki daya, sai ya tunatar da su nauyin da ke kansu nab a yaransu tarbiyya nagari, da zai tsirar da yaransu daga fada wa cikin badalar da zai cutar da yaransu na rayuwarsu nay au da kuma na gobe.

A dai jawabinsa ya yaba wa al’ummar Dan Magaji na yadda suke ba ‘yan sanda goyon baya da kuma shawarwarinsu da suka zama silar samar da ingantaccen zaman lafiya a wannan yanki na Dan Magaji, ya ce, ya na fatan hakan zai ci gaba.

Tun farko a jawabinsa, babban jami’in da ke kula da gundumar Dan Magaji, Alhaji Buhari Bello, ya nuna matukar jin dadinsa da yadda kwamandan ‘yan sandan ke aiwatar da ayyukan da aka dora ma sa, ya ce, salon mulkinsa ya zama darasin da suke dauka a kullun, da ya haifar da samar da zaman lafiya a daukacin shiyya ta daya baki daya.

Sauran wadanda suka yi jawabi a wajen wannan ziyara ta kwamandan ‘yan sandan a shiyya ta daya, sun hada da Sarakunan Dan Magaji  da Unguwar Dankali da ma su unguwanni da suke wannan gunduma ta Dan Magaji,

kungiyoyin sufuri da kungiyar da suke aiki a tsakanin ‘yan sanda da al’umma [PCRC] da kuma kungiyar filani ta Miyetti Allah na karamar hukumar Zariya.

Exit mobile version