Kwamishinan harkokin ‘yan kasashen waje da yawon bude ido gami da al’adu ta jihar Anambra, Dakta Christian Madubuko, ya yi murabus daga wannan mukamin.
Wasikar barin aikin na Maduboko mai dauke da kwanan wata 11 ga Disamban 2020 wacce ta shiga hannun ‘yan jarida a jiya a garin Akwa.
Tsohon kwamishinan ya yi zargin cewa ana tafka cin hanci da rashawa wanda hakan ne ma ya kai shi ga daukan matakin ajiye aikin, tare da kiran gwamnan jihar Willie Obiano da ya tashi tsaye domin kare martabar gwamnatinsa.
Rahotonni sun yi nuni da cewa Mista Madubuko ya shafe tsawon shekaru kusan uku a matsayin Kwamishinan masa’antu da kasuwanci, tare da Kwamishinan hanyoyi da layin dogowa.
“A dalilin yaki da cin hanci da rashawa, daidaikun mutane na rike kudin harajin jihar, wasu sun yi ta rubuta takardun korafe-korafe a kaina su na aike wa gwamna, a bisa kokarina na tabbatar da an daina cinye dukiyar jihar.
“Sun zarge ni musguna wa jam’iyyarmu ta APGA, su na shawartar gwamnan da ya cire ni kafin na illata jam’iyyar,” ya shaida.
Madubuko ya yi zargin cewa masu tafka ta’asar sun sha kokarin ba shi cin hanci domin ya daina tona musu asiri.
“Ya bayyana karara, a duk lokacin da kake kokarin yaki da hanci hanci da rashawa, to kana yaki ne da wasu da dama.”
Ya ce, ya zo jihar ne domin ya taimaka wajen gina jihar ba wai don ya tara dukiya ko wani shirin musguna ma wani ba.
Ya ce, sun sha kai masu badakala da kudin haraji kotu domin a dauki matakan da suka dace.
Ya kara da cewa a bisa hakan jama’a da dama sun hareshi da kokarin cutar da shi gami da neman kai masa farmaki a bisa yaki da yake yi wajen ganin an taskace dukiyar jihar ta sashin haraji.
Daga bisani ya nemi gwamnan jihar da ya fa tashi tsaye ya kara sanya ido kan yadda ake tafka cin hanci da rashawa a gwamnatinsa.
Da ya ke maida martani kan wannan matakin, kwamishinan yada labarai na jihar Mista C Don Adinuba, ya shaida cewar gwamnati ta amshi wasikar ajiye aikin Madubuko.
Adinuba, bai ce uffan ba kan zarge-zargen rashawa da Madubuko ya yi.
Sai dai shi tsohon kwamshinan ya nuna matukar farinsa da kasancewarsa dan jam’iyyar APGA kuma ya ce har yanzu a kan wannan matakin yake, yana mai nuna fatan cewa bai son ganin gwamnatin jihar ta gaza nasara ko wani ya zubda mata kima.