Rabiu Ali Indabawa">

Kwamishinan Ilimin Jihar Kano Ya Jinjina Wa Daliban Firamare Da Kungiyar KISS

Kwamishinan ilimi na jihar Kano Alhaji Sanusi Sa’idu Kiru, Majidadin Kiru ya lashi takobin ganin duk wani dan jihar Kano ya samu ingantaccen ilimi, yayi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a santocin da daliban firamare ke rubuta jarabawar tafiya Sakandire ne a fadin jihar ta Kano.

Kwamishinan ilimin ya kara da tambayar daliban ko da me son ya tafi sekandire ta kwana wato boarding school a turance, yayin da su kuma daliban mafiya yawanci maza ne suka daga hannayensu sama wanda yake nuna alamar sun amince za su tafi makarantun kwana, a cikin muryar ta barkwanci Mai girma kwamishinan ya ce wato ku ‘yan mata kun fi son aure ke nan ko?, yayin da suka ba shi amsa da cewa Baba ilimin yara mata shine a kan gaba, kwamishinan yayi dariya ya ce musu gwamnatin Babanmu Ganduje ta mike tsaye tsayin daka domin ganin ta samar muku ingantacce ilimi a jihar mu ta Kano mai albarka, ba ma iya makarantar firamare ko Sekandire ba har ma da makarantun gaba da sakandire.
Mai girma kwamishinan ilimin ya rufe taron da kara godewa dalibai, malamai da ma’aikatan ilimin jihar Kano da suka shirya jarabawar shiga makarantar gaba da Firamare wacce aka fi sani da sunan Common Entrance Edamination kuma a nuna gamsuwar sa akan yadda aka gudanar da jarabawar.
A bangare guda kuma Kwamishinan bai tsaya a nan ba har sai da yakarbi bakuncin matasa ‘yan wasan kwallon kafa ta kiru Soccer Stars United wacce aka fi sani da suna KISS.
kungiyar kwallon kafar ta Kiru Soccer Star ta kawo masa ziyarar ban girma ne domin nuna goyon bayan su da yadda Kwamishinan ilimin jihar ta kano ya jijirce domin ganin matasa maza da mata sun samu ci gaba ta fuskar ilimi da harkokin wasanni a jihar, kungiyar dai ta samu jagorancin shuwagabannin ta kamar irin su Koci-kocin kungiyar, inda Koci Sa’idu wanda akafi sani da suna Rambo ya jangoranci tawagar.
A jawabinsa shi wanda ya samu damar jagorancin ziyarar wato Koci Rambo, ya jaddada godiyar su da goyon bayan da Kwamishinan Ilimi na jihar Kano ke bai wa matasa domin ci gaban wasanni a jihar Kano kuma ya kara da cewa suna matukar mika godiyar su ga kwamishin domin gudunmuwar da ya basu ta rigunan kwallon kafa da aka fi sani da suna Jessy a turance da kuma kwallayen kafa da aka fi sani da suna ball a turance, kuma sun ci alwashin ba shi gudunmuwa domin ganin Jihar Kano ta cigaba.

Exit mobile version