Mai martaba Sarkin Koton karfe( Ohimege Igu), Alhaji Abdulrazak Gambo Isah Koto a ranan juma’a 25 ga watan disambar 2020,ya nada kwamishinan kudi da tsare tsaren tattalin arziki na jihar Kogi, Alhaji ( Mukaddam) Idris Asiwaju Asiru a matsayin Turakin Koton Karfe.
Bikin wanda aka gudanar a fadar mai martaba Sarkin bayan sallar juma’a, ya samu halartar manyan baki daga sassa daban daban na kasar nan.
Kwamishina Asiwaju yana daya daga cikin fitattun mutane 37 da suka ci gajiyar nadin sarautu daban daban da Sarkin na Koton Karfe, Alhaji Abdulrazak Gambo Isah Koto ya nada kuma bikin yayi armashi matuka gaya.
Da yake jawabi a wajen nadin saraurar, mai martaba Sarkin Koton Karfe ( Ohimege Igu) wanda ya bayyana farin cikinsa ganin yadda fadarsa ta cika makil da jama’a babu masaka tsinke, domin kashe kwarkwatar idanunsu yadda bikin zai gudana, yace ya nada kwamishinan kudi da tsare tsaren tattalin arziki na jihar Kogi, Alhaji Idris Asiwaju Asiru a matsayin Turakin Koton Karfe ne saboda dimbin gudun mawar da yake bayarwa wajen ci gaba da kuma habbakar tattalin arzikin jihar Kogi, wadda a cewarsa bashi misaltuwa.
Sarkin yace da wannan nadi na Turaki, a yanzu Alhaji Idris Asiwaju Asiru ya zama daya daga cikin masu rawanin Sarkin na Koton Karfe.
Da yake mayar da jawabi kadan bayan nada a matsayin Turakin Koton Karfe, kwamishinan kudi da tsare tsaren tattalin arziki na jihar Kogi, Alhaji( Mukaddam) Idris Asiwaju Asiru ya bayyana farin cikinsa da ganin wannan rana, wadda a cewarsa rana ce da ba zai taba mantawa a rayuwarsa ba.
Alhaji Idris Asiwaju Asiru ya kuma godewa mai martaba Sarkin Koton, Alhaji Abdulrazak Gambo Isah Koto a bisa karamma shi ta hanyar nada shi a matsayin Turakin Koton Karfe, yana mai jaddada cewa nada shi sarautar zai kara masa kwarin gwiwa da karfin bautawa jihar Kogi a matsayinsa na kwamishinan kudi da tsare tsaren tattalin
arziki na jihar.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’ar jihar Kogi dasu ci gaba da baiwa gwamnatin Alhaji Yahaya Bello goyon baya a kokarin data keyi na kai jihar da al’ummarta tudun na tsira.
A karshe Alhaji Idris Asiwaju Asiru ya godewa dukkan wadanda suka yi ruwa, suka yi tsaki wajen ganin nadinsa a matsayin Turakin Koton Karfe yayi nasara.
Sabon Turakin Koton Karfe, Mukaddam Idris Asiwaju Asiru da Uwargidansa kadan bayan nada shi