Kwamishinan Muhalli Alhaji Hamza Sule Wamban Faskari Alkhairi Ne Ga Al’ummar Jihar Katsina

Faskari

Daga Abdullahi Sheme,

Wanene Alhaji Hamza Sule Faskari shi ne kwamishinan Muhalli na jihar Katsina a halin yanzu kuma wamban faskari wanda maigirma Gwamnan jihar yakara nadashi kwamishina karo na biyu a karkashin Gwamnatin  Alhaji Aminu Bello Masari Dallatun Katsina  Matawallen Hausa matashin kwamishina ne mai jini a jiki wanda yake taimakon Al”umma hade da matasan jihar domin su rage zaman kashe wando da inganta rayuwar matasan da tallafama marayun jihar da daukar dawainiyar yara da manya marasa lafiya  wadanda basu da galihu zuwa manyan asibitocin dake zariya kano da Katsina da sauran asibitocin kudi don ceto rayukansu. Kwamishina Alhaji Hamza Sule yana daya daga cikin kwamishinonin jihar masu taimako a Gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari mafi yawan Al”umar jihar sun ce tun lokacin da a ka kirkiro jihar a cikin shekarar 1987 ba a taba samun kwamishinan dake taimakon Al”uma ba kamar Wanban na Faskarin ko a shekarar data gabata 2020 ya rabama matasan jihar manyan Babura masu tayoyi 3 wadanda a ke daukar kaya dasu sama da guda 100 kudin kowanne Babur ya kai kusan Naira 700,000 wanda hukumar NEWMAP a karkashin ma aikatarshi ta bayar dasu  da kokarinshi na wajen su dogara da kansu su kama sana”a sannan ya samarma matasan Faskari da Sabuwa da karamar hukumar Kankara ayyukan Gwamnati musamman yaran da suka kammala karatunsu  na digiri Wamban na Faskari bai tsaya a nan ba ko kwanannan ya dauki dawainiyar kananan yara wajen su 4  kai su asibiti  a kwai yaro daya a chediyar danliyo dake karofi a cikin garin Funtuwa da wasu yaran a garin Maigora da ‘Yankara  da wasu a cikin garin Faskari duka a cikin karamar hukumar Faskari mutanen da Kwamishina Alhaji Hamza Sule ya dauki dawainiyarsu marasa shi zuwa asibitoci ya biya milyoyin  naira domin a yi masu aiki a sibitoci daban daban suna da yawa ko a farkon sabuwar shekaran nan da muka shiga ciki ya bayar da kudade jali ga matasa da mata da kungiyoyi da ban da ban a kananan hukumomin faskari da Sabuwa sama da mutum 1000 domin  su dogara da kawunansu kazalika yana taimakon gidajen da akayi rashi inda yake kai ziyarar ta’aziyya tare da taimakon gidajen da a kayi rasuwar wajen biyama mamacin bashi da kai taimakon abinci Wamban na faskari mutum  ne mai tausayi da taimakon dattawa mabarata  shiyasa mutane keyi mashi kirarin cewar Wambai Alkhairi ne ganinshi Rabone kuma hakane wakilinmu ya ziyarci karamar hukumar Sabuwa inda ya zanta da wani bawan Allah  maisuna malam Mustafa Damari ya yaba da irin halayen Alhaji Hamza Sule yadda yake taimakon Al umma a ko da yaushe taimako na domin Allah kuma kusan a lokaci daban daban yana ziyartar mutanen wannan karamar hukuma ta sabuwa ya ce wannan bawan Allah Kwamishinan basu zabeshi wani mukami ba amma yana taimakon Jama”a ako da yaushe don haka ya yi kira gareshi da ya daure yafito ya nemi wata babbar kujera a shekarar 2023 saboda zabenshi a wata kujera Alheri ga Al”ummar jihar Katsina harma da kasa baki daya Allah kadai yasan yawan Jama”ar da za su amfana da shi haka take ga sauran Mutanen da wakilinmu ya zanta dasu a kananan hukumomin Faskari da Kankara da Kafur da karamar hukumar Daura da Funtuwa da sauran wadansu jama”a daga kananan hukumomi da yawa a fadin jihar a karamar hukumar Funtuwa wakilinmu ya zanta Sajan Haruna Muhammed mairitaya tsohon shugaban kungiyar direbobin sufuri ta kasa reshen jihar Katsina kuma shine sabon  shugaban kungiyar direbobin sufurin na jihohin Arewa maso yamma jihohi 7 da Alhaji Abdullahi Yusuf mai zabo daga karamar hukumar kafur da tsohon kansila Alhaji Ibrahim Kasko daga Kankara da Alhaji Rabe maye mazoji daga karamar hukumar Daura da sauransu duk suyaba da halayen wamban faskari dafatan Allah ya saka mashi da mafi Alkhairi da ganan sukayi kira ga sauran yan siyasar jihar dama na kasa baki daya suyi koyi da halin kwamishinan muhalli na jihar Katsina daga karshe sun godema maigirma Gwamnan jihar Alhaji Aminu Masari Dallatun katisinawa matawallen hausa wajen kara nadashi kwamishina karo na biyu sun godema Gwamnan yadda yaciyar da jihar gaba wajen gabatar da manyan aiyuka ga mutanen jihar baki daya.

Exit mobile version