Sagir Abubakar" />

Kwamishinan Ruwan Jihar Katsina Ya kaddamar Da Wasu Na’u’rorin Ruwa

Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Katsina ya duba fanfunan tura ruwa na zamani guda shidda wadanda aka samar a tashar samar da ruwa da ke kofar kaura a cikin garin Katsina.

Gwamnatin Jihar Katsina ce ta samar da fanfunan da yawan kudin su ya kai fiye da Naira Miliyan dari Hudu. Alhaji Musa Adamu Funtua, ya ce an samar da fanfunan ne domin magance matsalar rashin ruwa a cikin garin Katsina.
Ya ce, gwamnati ta kuma kashe fiye da Naira Miliyan dari Shidda domin gyaran tashar samar da ruwa ta kofar kaura, samar da na’urorin tura ruwa na zamani da sauran kayan gyara duk domin inganta samar da ruwa a Jiahr nan.
Kwamishinan ya bayyana godiyarsa ga gwamnati da kuma dan kwangilar bisa samar da fanfunan duk da annobar corona da kasar nan ke ciki. Tun da farko, shugaban hukumar samar da ruwa na jiha Alhaji Ibrahim Dasuki ya bada tabbacin cewa ruwa zai samu a jihar Katsina.

Exit mobile version