Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Abdulrahman yayi kira ga iyaye dasu hadawa ‘ya’yansu ilimin boko dana addinin Musulunci, ta yadda za’a samu Shugabanni nagari a kowanne fanni na rayuwa.
Kwamishinan yayi kiran ne awajen bukin yaye daliban da suka haddace Alqur’ani maigirma a shekara daya na Makarantar Nurut Tilawah dake Zaria a ranar Lahadin data gabata. Ya kara dacewa, “zaiyi kyau a samu Jami’an ‘yan sanda, Kwastam, sojoji da ‘yan sandan farin kaya Mahaddata Qur’ani kamar irin Alarammanmu DSP Khalid Wada Khalid ” yayi jinjina ta musanman ga Iyaye da malaman yaran don jajircewarsu wajen ganin sun samu haddan Alqur’ani.
Tunda farko Shugaban Taron Maigirma Tsohon Ministan Ilimi kuma Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau, yaja kunnen yaran wajen ganin sunci gaba da neman sauran ilmoma da suka shafi addinin musulunci da aiki da shi.
A nasa jawabin Shugaban Makarantar Sheikh Nuruddeen Umar Tahir, yace Makarantar nada tsarin na bude shashin karatun boko don ya zama dalibai sun hada duka bangarorin.
Taron ya samu halartar wakilin Shugaban cibiyar haddan Alqur’ani ta duniya Sheikh Abdallah Bin Ali Basfar, wakilin Gwamnan jihar Kaduna, wakilan Sarakunan Zazzau, Suleja da Abaji, dade sauran manyan baki da dama.