Khalid Idris Doya" />

Kwamishinan ’Yan Sandan Bauchi Ya Yi Bikin Kara Wa Jami’ansa 135 Girma

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Ali Janga ya lika shaidar karin girma wa manya da kananan jami’an ‘yan sanda su 135 da suka samu karin girma zuwa matakai daban-daban na aikin dan sandan Nijeriya.
Wannan bikin sanya alamin karin girma ga jami’an na zuwa ne bayan da hukumar ‘yan sanda ta kasa ta amince da karin girman da kuma fitar da jerin wadanda ta yi wa karin girman daga cikin jami’an ‘yan sandan.
LEADERSHIP Ayau ta nakalto cewar wadanda aka sanya musu tabbacin karin girma sun kunshi masu mukaman masu taimaka wa kwamishinan ‘yan sanda zuwa matakin mataimakan Kwamishina su uku 3; masu mukamin mataimakan Sifuritandan dan sanda (SP) su ma su uku an daukaka musu lifafarsu zuwa mukamin Sifitandan dan sanda.
Sauran sun kunshi ‘yan sanda masu mukamin mataimakan Sufuritandan (ASP) su goma sha uku 13 da aka daukaka matsayarsu zuwa mukamin mataimakan Sufuritandan; sai kuma wasu ‘yan sanda masu mukamin Insifekta su 116 da aka daukaka matsayarsu zuwa mukamin masu taikama wa Sufuritandan (ASP).
Shi dai Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Bauchi, Ali Janga ya jagoranci sanya wa jami’an da lifafarsu ta cilla daga matakin da suke a da baya zuwa matakin aiki na gaba ne a jiya Talata a dakin taro na Rundunar ‘yan sanda da ke ‘Police Officers’ Mess, Bauchi’, wanda ya samu dafawar mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda a sashin kudi da gudanarwa na Rundunar wajen sanya alamin shaidar a jikin rugunar aikinsu.
Da yake gabatar da jawabi a wajen sanya wa jami’an shaidar karin girma, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Ali Janga ya shaida cewar karin girman an gudanar da shine bisa cancanta da kwazon kowani dan sanda, don haka ne ya jawo hankalin jami’an da suka samu karin girman da su yi amfani da damar da suka samu wajen kara azama da kwazo a fagen aikinsu, domin a cewarsa yin hakan ne zai kara musu zuwa wani mataki, ya kuma nusar da cewar duk wanda ya gaza nuna kwazo a wurin aikinsa zai dankare a matsayin da yake.
A cewar shi; “Ina mai amfani da wannan damar wajen yaba wa hukumar ‘yan sanda ta kasa a bisa amince da karin girman da ta yi wa jami’an ‘yan sanda. Ita hukumar ‘yan sanda ‘Police Serbice Commission’ ta gudanar da karin girman ne bisa cancanta da kuma tabbatar da aiwatarwa, sannan ta fitar da jerin sunayen wadanda karin girman ya shafa.
“Daga cikin jami’anmu da suke karkashin shalkwatan Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi da karin girman ya shafa sun hada da ACP da suka koma DCP su uku, masu mukamin DSP da suka samu karin girma zuwa SP su ma su uku, sai kuma masu mukamin ASP da suka samu cillawa zuwa mukamin DSP su 13; sai kuma jami’an ‘yan sanda masu mukamin Insifekta da suka samu haurawa zuwa mukamin ASPs su 116,” Inji Kwamishinan.
Kwamishinan ‘yan sandan, ya kalubanci wadanda suka samu karin girman da cewar wannan wani hanya ne suka samu domin kara ninka kokarinsu domin tabbatar da aikin dan sanda na gudana yadda ya dace.
Ya kuma taya su murna da wannan nasarar da suka samu; “Muna tsammanin kwazo da hazaka daga wajen dukkanin wadanda karin girman na shafa, muna fatan za ku ribanya kokarinku da kwazonku a wuraren aiyukanku,” A cewar shi.
Daga nan ne kuma ya nanata cewar Rundunarsu da hadin guiwar sauran bangarorin tsaro za su ci gaba da tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’an jihar Bauchi a kowani lokaci.
Da yake jawabinsa na godiya a madadin jami’an da aka kara wa girman, babban jami’in dan sanda a caji ofis din ‘yan sanda da ke Dambam (DPO) SP Abdulmumini Musa, ya gode wa hukumar gudanarwa da hukumar da ke kula da rundunar ‘yan sandan Nijeriya a bisa wannan karin girman da suka musu, yana mai shan alwashin cewar za su yi amfani da damar da ke gabansu wajen daukaka darajar dan sanda da kuma kyautata aiki a duk inda suka samu kawukansu.
Wakilinmu ya kuma shaida mana cewar an gudanar da kasaitaccen walimar taya murna ga jami’an da suka samu karin girman, inda suka kasance cikin murna da farin ciki, kana wasu daga cikin wadanda aka yi wa karin girman sun samu takiyar iyalansu wajen shaidawa da tabbatar da sanya alamin karin girman a wajen bikin da aka yi musu.

Exit mobile version