Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rundunar ‘yan sanda ta kama wasu hadiman gwamnati da zababbun ‘yan siyasa na Karamar Hukumar Ohaukwu. Kwamishina ‘yan sandan Jihar Ebonyi ne ya shiga har wurin taron masu ruwa da tsaki ya fito da mutanen tare da tafiya da su. Mataimakin Gwamnan Jihar Ebonyi ne ya kira taron sulhu tare da gayyatar masu ruwa daga yankin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ebonyi, Aliyu Garba, ya kama Shugaban Karamar Hukumar Ohaukwu, Clement Odah, da mamba mai wakiltar Karamar Hukumar a majalisar dokokin jihar, Chinedu Awo, bisa zarginsu da hannu a kisa da barnar dukiya da aka yi a yankin.
Kazalika, rundunar ‘yan sanda ta kama wasu sauran hadiman gwamnati da masu ruwa da tsaki a yankin har su 30, wadanda suka hada da shugaban kungiyar ci gaban Effium, Sunday Agbo, da abokin burminsa Eucharia Ogwale. Sauran wadanda rundunar ta sanar da kamawa sun hada da tsohon sakataren yada labaran gwamna, Emmanuel Uzor, wanda yanzu mai bawa gwamna shawara ne da kuma wani hadimin gwamna mai suna Emmanuel Igwe.